Hidimar ilimi ta haskaka Madawakin Daura

Madawakin Daura Injiniya Mustapha Bukar ne ya kafa makaranta da aka fara biyan Naira 100 a matsayin kudin makaranta. Wannan ne ya sanya ya shiga cikin mutanen da Allah ya azurta masarautar Daura da su, ta wajen assasa ayyukan alheri a fannoni da dama na rayuwar al’umma da a yau ake cin gajiyarsu. Sannan ‘ya’ya […]

Hidimar ilimi ta haskaka Madawakin Daura
Hidimar ilimi ta haskaka Madawakin Daura

Madawakin Daura Injiniya Mustapha Bukar ne ya kafa makaranta da aka fara biyan Naira 100 a matsayin kudin makaranta. Wannan ne ya sanya ya shiga cikin mutanen da Allah ya azurta masarautar Daura da su, ta wajen assasa ayyukan alheri a fannoni da dama na rayuwar al’umma da a yau ake cin gajiyarsu. Sannan ‘ya’ya da jikoki da za su biyo baya suma cikin yardar Allah za su ci moriyarsu. Hakika wannan hidima ta bunkasa ilimi da wannan basarake ya himmatu a kanta ta haskaka tauraronsa, tare da kara masa kimar daraja da mutunci a idon al’umma.

Idan muka waiwaya baya za mu ga yadda ya gudanar da aikinsa na gwamnati, za mu ga ya taka muhimmiyar rawa wajen gina wannan kasa Najeriya, musamman jihar Katsina a takaice. Ta fannin aiki sa kai da al’umma ke cin moriyarsu, akwai da dama da shi ne ya fara assasa su a masarautar Daura da a yau ake amfana da su.
Da farko ta fannin ilimin rayuwa Allah ya datar da shi ya karanci sashe mafi muhimmanci da rayuwar kowani abu mai rai, kai dama marar rai ta ta’allaka da shi watau ‘ruwa’. Madawakin Daura fitaccen injiniya ne, masanin albarkatun ruwa da ya samu kwarewa akan yadda ake samar da tsaftaccen ruwan sha. Kai har sai da ya rike mukamin Shugaban Sashen kula da albarkatun ruwa na Afirka (Chairman African Water Resources).
Ya fara aiki da ma’aikatar ruwa ta tsohuwar jahar Kaduna kafin kirkiro da Jihar Katsina a 1978. Ya kuma rike matsayin Majana Ayyukan a Hukumar Samar d aRuwan Shat a Jihar Kaduna, a karkashin tallafin Bankin Duniya. Da aka kirkiro Jihar Katsina a shekarar 1987, an nadashi Shugaban Hukumar Samar da ruwa ta Jihar Katsina. A haka dai, har ya kai ga matsayin Kwamishinan albarkatun ruwa na Jihar Katsina, inda ya kaddamar da aikin gina sababbin gidajen ruwa na dukkan kananan hukumomin da ke jihar, da kuma aikin inganta tsofaffin da ake da su. Daga bisani ya koma aiki da gwamnatin Tarayya, inda ya yi murabus a shekarar 2007. Madawaki ya kafa Gidauniyar Ilimi mai suna ‘DanBukar Education Foundation’ a shekarar 1991. Da kudurin bunkasa ingantaccen ilimi a Masarautar Daura. A shekarar 1992 Gwamnan Mulkin Soja na Jihar Katsina a waccan lokacin Col. Yahaya Madaki ya zo garin Daura ya aza harsashin ginin Madawaki Nasari da Firamare a matsayin makarantar Kudi ta farko a dukkan fadin masarautar Daura. Daga nan aka kafa a kananan hukumomin; Mai’adua da Zango da kuma baure. An fara biyan kudin makaranta Naira 100 a 1992 duk karshen zangon karatu, wanda aka dauki sama da shekaru sama da goma Madawaki shi ke cika kudin a aljihunsa duk karshen wata domin yin albashi da kuma sauran harkokin gudanar da makarantun.
A yau rukunin Makarantun danbukar sun yaye sama da Dalibai 1500, da za ka hada jumallar daliban da suka kammala karatun gaba da sakandire a garin Daura daga shekarar da danbukar ta fara yaye dalibanta a 1997 zuwa yau. To za ka samu daliban da su ka yi danbukar suna nema su yi kunnen doki a yawa, in za ka kwatantasu da wanda suka halarci Makarantun Gwamnati a tsawon wannan lokaci. Ya kafa karamar Sakandire a Daura, ya kuma gina katafariyar makaranta ta zamani a Abuja mai dauke da bangare uku: Nazare da Firamare da Sakandire da kuma Islamiyya da ake gudanar da harkokin ilimi. Madawaki ya kafa wurin koyar da na’urar kwamfuta ta farko a garin Daura, inda ake koyar da daliban makarantar danbukar da malamansu, da kuma sauran mutane masu sha’awar koyar ilimin. Sannan kuma ya kafa wurin sayar da littattafai da kayan aikin ofis, don dalibai su samu kayan koyon karatu masu inganci.
Hatta a fannin kasuwanci Madawaki ya ba da gidansa don kafa Bankin Manoma, wanda ya kasance Banki na biyu da aka kafa a Daura, bayan rushewar Bankin Arewa na farko a Daura. Shi ne mutum na farko da ya fara kafa masana’antar buga ruwan leda a Daura, kuma yana daga cikin wadanda suka fara kafa wurin sayar da bulo na suminti. Ya samar wa mutane ayyukan yi a ma’aikatu da dama da kuma kyakkyawar mu’amula da na kasa da shi, wanda wasu a yau sun sami daukaka a duniya. A jerin mutanensa akwai tsohon Shugaban Majalissar Wakilai Rt. Aminu Bello Masari da Rt. Hon Ya’u Gojo Gojo.
Irin wadannan mutanen da suka sha gwagwarmayar rayuwa, musamman ganin yadda suka himmatu wajen taimakon al’umma, lallai akwai bukatar su zama abin koyi ga al’umma. Kuma kafafen mu na yada labarai su rika tattaunawa da su, don masu tasowa su koyi wani abu daga dimbin basirar da Allah ya ba su. Za mu ci gaba da cin gajiyar irin wadannan gwaraza a cikin al’umma ne, matukar aka samu masu koyi da su, ko ma wadanda za su dora daga inda suka tsaya, har ma su fi su. Babban abin koyi dais hi ne hidima ga ilimi, ta yadda za mu rage zaune gari banza, da masu gararamba a tituna. Tunda ko ba komai idan har ka ilimantar da al’umma, to ka gina tunaninsu, ta yadda za su sama wa kansu makoma tagari.

Injiniya Jibril Abdul Daura
Tsohon dalibi ne na Makarantar Danbukar Daura
08038997861, 08022997043.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu