Hidindimun Gizagawa

Taron Gizagawan Najeriya 2019 A yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa game da Taron Gizagawan Najeriya na bana, inda insha Allahu za a gudanar da shi a zauren taro na Kwalejin Barewa da ke Zariya a Jihar Kaduna, a ranakun 14 zuwa 15 ga Diasamban nan. A bana taron zai samu halartar babban mai jawabi, […]

Hidindimun Gizagawa

Malam Nura Adamu Ahmed

Taron Gizagawan Najeriya 2019

A yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa game da Taron Gizagawan Najeriya na bana, inda insha Allahu za a gudanar da shi a zauren taro na Kwalejin Barewa da ke Zariya a Jihar Kaduna, a ranakun 14 zuwa 15 ga Diasamban nan. A bana taron zai samu halartar babban mai jawabi, Farfesa Ibrahim Malumfashi, na Jami’ar Jihar Kaduna, wanda zai gabatar da makala game da Gudunmawar Jaridun Hausa ga Al’umma. Kuma taron zai gudana na ne, musamman domin tunawa da daya daga cikin iyayen kungiyar, marigayi Malam Mahmoon Baba Ahmad.

Sakon Bagizagen Mako

Bakonmu na wannan mako, shi ne tsohon Shugaban Riko na Kungiyar Gizagon Najeriya, Nura Adamu Ahmed (08065429888). A sakonsa ga daukacin Gizagawa, yana cewa:

Assalamu alaikum, Gizagawan Zumunci, Gizagawan Najeriya. Gaisuwa, jinjina da fatar alheri wanda ba ya yankewa ga Madugun Zumunci, Malam Bashir Yahuza Malumfashi da kuma jajirtaccen shugabanmu Malam M. K. Adam Gombe, tare da haziƙan ’yan majalisarsa da suka dage wajen gudanarwa da ci gaban harkokin Gizago; musamman a wannan kafa ta jaridarmu Aminiya mai farin jini. Allah (SWT) Ya ƙara muku himma, kwazo da basirar ɗaukaka wannan ƙungiya zuwa gaba, amin.

Bayan haka ina son in yi amfani da wannan dama wajen jan hankalin ’yan uwana Gizagawa, cewa duk wanda yake son sadar da zumunci irin wanda Musulunci ya tsara, dole ne ya ajiye kyashi, kasala da matse hannu. Mu zama jajirtattu, masu dagewa da bude bakin aljihu don ganin wannan kungiya tamu mai albarka ta ci gaba, ta bunkasa, ba ma iya Najeriya da Afirka kadai ba, har da duniya baki daya. Allah Ya sa wannan haduwa tamu ta zamo ita ce silar shigarmu Aljanna. Amin, na gode.

 

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos