Hidindimun gizagawan zumunci
Kamar yadda Gizagawa suka saba aikin alheri, a makon da jiya ne Gizagawan Jihar Gombe suka kai ziyarar dubiya ga daya daga cikin mambobinsu, mai suna Malam Adamu Sambo, wanda aka yi wa aikin ido. Ayarin Gizagawan ya isa gidan Malam Adamu da yammacin ranar Asabar, bisa jagorancin Shugaban Gizago Reshen Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu […]
Kamar yadda Gizagawa suka saba aikin alheri, a makon da jiya ne Gizagawan Jihar Gombe suka kai ziyarar dubiya ga daya daga cikin mambobinsu, mai suna Malam Adamu Sambo, wanda aka yi wa aikin ido.
Ayarin Gizagawan ya isa gidan Malam Adamu da yammacin ranar Asabar, bisa jagorancin Shugaban Gizago Reshen Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Korau. Cikin ayarin har da Shugaban Gizago na Kasa, Muhammd Kabir Adam (MK). Daga nan ayarin ya wuce wata dubiyar zuwa Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Gombe (FMC), inda ya duba Shugaban Kungiyar Rayaas, reshen Jihar Gombe, Malam Ibrahim Affan; wanda ya hadu da hadarin mota.
A madadin daukacin Gizagawan Najeriya, muna addu’ar Allah Ya ba su lafiya, Ya sa kaffara ce, amin.
Sakon Bagizagen Mako
Bakonmu na wannan mako, shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Gizago na Najeriya, Malam
Abdullahi Alkwatanawi (08066666653) mai lambar kungiya (GZG-142-OGN). Ko mene ne sakon Mataimakin Shugaban na Gizagawa? Ga abin da yake cewa:
Assalamu alaikum! Gizagawan Zumunci tare da fatan alheri a gare ku!
Da farko ina kira ga Gizagawa mu sa tsarkakakkiyar niyya, mu jaddada zumunci ta hanyar jinkan juna da taimakon juna. Kada mu gajiya da wannan zumunci iyakar iyawarmu!
Haka kuma mu ci gaba da kai ziyara asbitoci domin duba marasa lafiya, tare da kai irin wannan ziyara ga gidajan marayu da na wakafi, domin tallafa musu da duk abin da ya sauwaka!
Daga karshe ina kira da babbar murya ga shugabannin Gizago na jhohi da su ba da himma sosai wajen kiran taro a jihohin da suke jagoranci!