Hikayata: Dalibar Faransanci ta lashe gasar adabin Hausa

Matashiyar mai shekara 18 a duniya ta wallafa littattafai 5 duk da ana hana ta rubutu a gida

Hikayata: Dalibar Faransanci ta lashe gasar adabin Hausa

An bayyana Aishatu Musa Dalil, wacce daliba ce mai karantar harsunan Ingilishi da Faransanci a jami’a, a matsayin gwarzuwar Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta BBC Hausa ta bana.  

Dalibar mai shekara 18 da haihuwa ta yi nasarar lashe Gasar ne da labarinta mai suna “Hakkina” wanda ya hakaito yadda mijin mahaifiyar wata yarinya ya yi mata fyade.

“Lura da yadda mata wadanda aka yiwa fyade da kyar za ka ga maza na auren su… suna fuskantar kalubale a rayuwarsu”, inji Aishatu.

A wata hira da ta yi da Aminiya gabanin sanar da ita a matsayin wacce ta lashe gasar, marubuciyar ta ce burinta  shi ne ta zama daya daga cikin manyan marubutan duniya da suka yi fice.

“Ina son isar da sako a duk duniya tare da shiga sahun marubutan duniya, a san ni tare da karanta rubutuna a ko’ina ba iya Najeriya kadai ba,” inji ta.

Matashiyar ta bayyana cewa duk da kalubalen da take fuskanta na cewa a gidansu ba a son ta mayar da hankali wajen rubutun kagaggun labarai, a hakan ta rubuta wannan labari da ya sanya ta zamo gwarzuwa a gasar.

Ta kara da cewa ta fara rubutun Hausa a shekarar 2018 lokacin tana da shekara 15 da haihuwa. kuma a halin yanzu tana da bugaggun littattafai guda biyar.

A karshe ta bayyana cewa wannan nasara tamkar mafarin cigaba ne a rayuwarta kuma a nan gaba tana fatan ta samu cigaban da ya fi haka.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja