Hikimar ango
Wani ango ne ana walimar bikinsa, ’yan uwa da abokan arziki duk sun taru. Bayan an kammala sai aka ce ango ya tashi ya yi jawabin godiya. Ango ya ce: “Godiya ta musamman ga Malam Sani Tudun Kaure dillalin gidaje, wanda ya ba mu aron inda za mu zauna, kafin mu samu haya. Ba zan […]
Wani ango ne ana walimar bikinsa, ’yan uwa da abokan arziki duk sun taru. Bayan an kammala sai aka ce ango ya tashi ya yi jawabin godiya. Ango ya ce: “Godiya ta musamman ga Malam Sani Tudun Kaure dillalin gidaje, wanda ya ba mu aron inda za mu zauna, kafin mu samu haya. Ba zan taba mantawa da Hajiya Shafale mai adashi ba, wadda ta ba ni daukar farko na kai kudin aure. Godiya ga Asabe dillaliya, wadda ta ba mu bashin atamfofi da shaddodi da muka sa a lefe. Allah Ya saka wa kanwata Habiba, da taimakonta ne na fita kunya don kuwa ita ce ta ba ni aron akwatunan lefenta, aka sa kayan a ciki. Allah Ya bar zumunci, Ya ba mu ikon cika alkawuran da muka dauka. Haka kuma ba zan manta da Atiku mai wanki da guga ba, shi ya ba ni aron kaya har na fita kunya. Mun gode, Allah maida kowa gidansa lafiya.”08133477778