Hikimar Bazazzagi

Wata rana wani Bazazzagi da abokinsa Bakano suna zaune waje daya kuma wajen sana’arsu daya. Wata rana sai wani abu ya hada su rigima a tsakaninsu. Rigimar har ta kai su kotu. Alkali ya tambayi kowa kuma kowa ya yi bayani. Sai alkali ya ji cewa ashe ma daga wasa ne sai rigimar ta tashi. […]

Hikimar Bazazzagi
Hikimar Bazazzagi

Wata rana wani Bazazzagi da abokinsa Bakano suna zaune waje daya kuma wajen sana’arsu daya. Wata rana sai wani abu ya hada su rigima a tsakaninsu. Rigimar har ta kai su kotu. Alkali ya tambayi kowa kuma kowa ya yi bayani. Sai alkali ya ji cewa ashe ma daga wasa ne sai rigimar ta tashi. Hakan ta sa alkalin ya ce to dukkansu ya yi musu afuwa a sakamakon fadin gaskiya da suka yi ba tare da sun wahalar da kotu ba. Ya ce kuma ya ba su dama kowanne ya zabi irin hukuncin da yake so a yi masa. Sai Bakano ya ce yana so a yi masa bulala 10 amma a sanya masa filo a bayansa kafin a yi masa bulalar. Alkali ya ce a yi masa yadda ya ce. Aka yi wa Bakano bulala 10 a kan filo, bai ji komai ba. Sai aka zo kan Bazazzagi, sai ya ce shi yana so a yi masa bulala 100 amma a dora masa Bakano a bayansa kafin a yi masa bulalar. Alkali ya ce a yi masa yadda ya ce. Ai kuwa aka sa Bakano a bayan Bazazzage, aka yi masa bulala 100. Bazazzage bai ji komai ba. Shi kuwa Bakano jikinsa ya yi rudu-rudu saboda bulala.
Daga Nura Suleja, 09027377656