Hikimarka jarinka: Tasirin marubuci a cikin al’umma

  Sanin kowane kowace halitta da irin baiwar da Allah Ya ba ta, haka a cikin halittun sai Allah Ya fifita dan Adam a bayan kasa ba don komai ba sai da ilimi. In muka dubi tarihin kakanmu Annabi Adam (AS) bayan halittarsa da hura masa rai sai Allah Ya sanar da shi sunayen duk […]

Hikimarka jarinka: Tasirin marubuci a cikin al’umma
Hikimarka jarinka: Tasirin marubuci a cikin al’umma

 

Sanin kowane kowace halitta da irin baiwar da Allah Ya ba ta, haka a cikin halittun sai Allah Ya fifita dan Adam a bayan kasa ba don komai ba sai da ilimi.

In muka dubi tarihin kakanmu Annabi Adam (AS) bayan halittarsa da hura masa rai sai Allah Ya sanar da shi sunayen duk wani abu da ke bisa doron kasa. Da wannan ne Allah Ya umarci mala’iku su yi masa sujada inda a nan ne Shaidan (Iblis) ya yi tawaye saboda hassada daga karshe Allah Ya sanya shi a cikin batattu shi da mabiyansa har zuwa Ranar Sakamako.

In muka lura a duniyar ilimi Allah Ya fifita malamai a kan sauran gama-garin al’umma amma bisa sharadin in ba su sayar da ilimin nan da Allah Ya ba su ba.

Haka da za mu dubi tarihin manyan malamai magabata irin su Imamu Malik sun yi gwagarmaya da gwamnatocinsu inda suka kare da shiga gidan yari don kawai sun ce a bi dokar Allah ko a bi ka’ida.

To haka marubuci yake a wannan al’umma da wannan karni da muke ciki ta yadda yake da gagarumar rawar da yake takawa don kyautata alaka mai kyau a tsakanin hukumomi da al’ummomin da suke mulka, wanda  in har marubucin bai jajirce ba ya cire kwadayi sai ka ga sakon ba zai kai inda ake nufi ba.

A wani bangaren marubuci kamar dan jarida yake wanda yake taka rawa wajen isar da sakon al’umma ga hukumominsu haka a wani bangaren za su isar da kyawawan ayyukan da su hukumomin ke aiwatarwa na raya kasa ko na bunkasar al’ummomin nan nata.

Daga karshe ina so marubuci ya dubi irin baiwar da Allah Ya yi masa ya yi amfani da ita don ciyar da jiharsa da kasarmu baki daya.

Tabbas ina alfahari da kasancewata marubuci abin tinkaho a cikin al’ummata.

Daga Sanusi Hashim Abban Sultana, 08065507271.