Hikimomin zama da miji (3)
Hikima ta 4: Girmamawa da Darajta Maigida: Wannan shi ne abu mafi girma da uwargida za ta yi wanda zai kawo mata daraja da daukaka a cikin rayuwar aurenta. Komai son da kike wa maigidanki, komai irin tsabtarki da iya kwalliya da rangwada da kwarkwasa, komai iya girkinki da kokarinki wajen ibadar aure, wadannan duk […]
Hikima ta 4: Girmamawa da Darajta Maigida: Wannan shi ne abu mafi girma da uwargida za ta yi wanda zai kawo mata daraja da daukaka a cikin rayuwar aurenta. Komai son da kike wa maigidanki, komai irin tsabtarki da iya kwalliya da rangwada da kwarkwasa, komai iya girkinki da kokarinki wajen ibadar aure, wadannan duk za su zube in ya kasance ba ki girmama maigidanki, ba ki ganin darajarsa, kina masa gani-gani, kina ganin ke bai tsare maki komai ba, da shi da babu duk daya saboda jin kai ko girman kai ko saboda wata matsala da ta faru cikin auratayyarku. Don haka kamar yadda kyakykyawar dabi’a take a matsayin tubalin ginin aminci da kwanciyar hankali, to girmama miji shi ne kwabin da ke hade bulon wannan ginin, wanda tabbas mun san in ba a like bulo ba, to cikin dan kankanin lokaci ginin zai wargaje. Ita girmamawa da darajtawa iri biyu ce kuma dole sai an aikata su tare sannan suke tasiri, in an yi daya ba a yi daya ba to kamar ba a yi komai ba ne.
Girmamawa da darajtawa ta badini: Shi ne ya kasance uwargida tana ji a zuciyarta da ma’aikatar hankalinta, girma da matsayin mijinta gare ta, cikin dadi ko tsanani; sanyi ko bazara; farin ciki ko bakin ciki; cikin fushi ko cikin walwala ba canji, wato canjin yanayi ba zai dauke ko ya rage daga girmamawar da take masa a cikin zuciyarta ba.
Girmamawa da darajtawa ta zahiri: Wannan tana da girma da fadin gaske domin tana shiga kowane bangare na rayuwar aure. Wato uwargida ta rika bayyanar da girmamawa da darajtawar da take ji cikin zuciyarta ga maigidanta a cikin dukan huldar rayuwar aurensu:
1. Wajen magana koyaushe ta kasance mai tauna kalaminta a zuci da ma’aikatar hankalinta kafin ya fade ta, koyaushe ta zama mai zabar kalmomi masu dacewa da yanayi kuma masu nuna ladabi da girmamawa, ko in tana cikin fushi ne, in har ta tabbatar ba za ta iya tauna kalamanta ba, to ta yi shiru shi ne mafi alfanu a kan ta fadi kalmar da ke bayyanar da raini ga maigida. Misali, uwargida tana cikin fushi game da maigida sai ya tambaye ta ‘ina hulata ?’ Da ta ce da shi ‘oho ban sani ba’ ko wasu kamomi makamanta to gara ta kalle shi a ido ta fuskance shi, ya ga tsananin fushin da ke rubuce a fuskarta, sai kawai ta yi shiru abinta. Wajen wasannin baka nan ma ko da wasa kada ta furta masa kalmomin masu daci da nuna raini gare shi; ta daure bakinta daga yawan nacin nuna masa laifuffukansa na ya yi kaza ko bai yi kaza ko bai iya kaza ba ko ya ki yin kaza. Lallai uwargida ta guji furta wadannan kalamai ga maigida, domin wadannan kalamai kamar tana cewa da shi ne: ‘kai kasashshe ne, ni na fi ka dabara, na fi ka kwarewa na fi ka hangen nesa.’ Furta irin wadannan kalamai masu bayyana rainin hankali da raina kokarin da maigida yake yi ba su da wani alfanu illa sassabe shukar soyayyar uwargida a zuciyar maigida da hana mata ruwa balle har ta girma ta yi yado ta bayar ga inuwa mai sanyi da ni’imtarwa.
2. Yana daga cikin girmamawa da darajtawa ga maigida in ya umarce ta ta yi in ya hana ta ta hanu; in ya ba ta shawara ta dauka koda ba ta amince da shawarar ba a zuciyarta.
3. Yana daga cikin girmamawa ga maigida kulawa da abubuwan da ba ya da nisantarsu da kulawa da abubuwan da yake so yawan aikata su, da tanadar musu abubuwan bukatar rayuwa bisa lokacin da ya bukace su ba sai ya yi jira ba.
4. Yana daga cikin girmamawa ga maigida ba shi hakuri idan an saba masa, da lallashi da kokarin kwantar da hankalinsa lokacin da yake cikin fushi ko bacin rai. kin ba shi hakuri yayin da aka saba masa na nuna halin ko-in-kula da nuna masa ba ya da wani matsayi, share shi lokacin da yake cikin fushi na nuna rashin kauna.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.