Hikimomin zama da miji (6)
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan hikimomin da uwargida za ta yi amfani da su don samun sauki da aminci cikin rayuwar aurenta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa […]
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan hikimomin da uwargida za ta yi amfani da su don samun sauki da aminci cikin rayuwar aurenta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Dabara ta 5: Koyi da magabata, ci gaba
Misali na biyu: Daga cikin wasiyyoyin da Umamah ta yi ga ’yarta Ummu Iyas ranar da za a kai ta gidan miji kashi 90 cikin 100 duk suna nuni ga dabi’un girmamawa, darajtawa da karrama miji:
Abdulmalik (Radhiyallahu Anhu) ya ce: “Lokacin da Auf bin Muhallim Ash-Shaibani, wani mutum mai tsananin daraja cikin Larabawan lokacin Jahiliyya ya aurar da ’yarsa Ummu Iyas ga Al-Haris Ibn Amr Al-Kindi, bayan an shirya za a kai ta gidan angonta, sai mahaifiyarta ta shigo gare ta domin yi mata nasiha inda ta ce da ita:
“Ya ke ’yata! In don kyawun dabi’a da kyakykyawan asali ne, to ba ki bukatar wannan nasiha, amma tunatarwa ce ga masu mantuwa kuma taimako ne ga ma’abuta hikima.
Ya ke ’yata! In da zai yiwu mace ta rayu ba tare da miji ba saboda arziki da bukatar mahaifi, to a cikin dukan mutane ke kika fi kowa cancanta ki rayu ba tare da miji ba; amma an halicci mata domin maza kamar yadda aka halicci maza domin mata.
Ya ke ’yata! Ga shi za ki bar gidan da kika girma a ciki, inda kika fara koyon ki taka ki yi tafiya, zuwa wani wuri da ba ki sani ba da abokin zaman da ba ki saba da shi ba; to ki sani, a dalilin aurenki da ya yi, ya zama shugabanki, ki zama kamar baiwa gare shi shi ma sai ya zama kamar bawa gare ki. Ki riki wadannan abubuwa guda goma daga gare ni sai su zame miki jari kuma abin tunatarwa:
Na 1 da na biyunsu shi ne ki kasance mai natsuwar zuciya a lokacin da kike tare da shi, ki saurare shi kuma ki bi umarninsa domin natsuwar zuciya na haifar da aminci saurare da biyayya ga miji yana daga cikin abubuwa masu dadi ga Allah (Subhaanahu Wa Ta’ala).
Na 3 da na hudunsu shi ne ki kasance koyaushe cikin kanshi mai dadi kuma cikin shiga mai kayatarwa, kada ya ga mummunan abu a tare da ke kuma kada ya shaki wani wari daga gare ki. Kwalli shi ne mafi kyawun abin yin kwalliya kuma ruwa ba turaren da ya kai shi kanshi.
Na 5 da na shidansu kuwa su ne ki tanadar masa abincinsa a kan lokaci kuma ki yi shiru lokacin da yake barci; domin zogin yunwa kamar kunar wuta yake kuma hana shi barci zai sa ya yi fushi.
Na 7 da na takwas dinsu shi ne ki kula da barorinsa da kuma ’ya’yansa, kuma ki kula da dukiyarsa, domin kulawarki ga dukiyarsa na nuna mutuntawa kula da ’ya’ya da barorinsa kuma na nuna iya jagoranci.
Na 9 da na gomansu kuma su ne kada ki sake ki bayyanar da sirrukansa, kuma kada ki sake ki ki bin daya daga cikin umarninsa, domin bayyanar da sirrukansa zai sa ba za ki tsira daga kaidinsa ba, in kuma kina saba umarninsa, zuciyarsa za ta cika da kiyayyarki.
Ki kiyaye, yake ’yata! Yin murna lokacin da yake cikin bacin rai, kada kuma ki nuna bacin ranki lokacin da yake cikin farin ciki domin na farkon na nuna rashin hangen nesa na biyun kuma zai bata masa rai.
Ki nuna masa girmamawa da darajtawa da yawa iya bakin karfinki, kuma ki yarje masa daidai iya karfinki domin hakan zai sa ya nishadantu da kasancewa da ke kuma ya nishadantu da yin hira da ke.
Ki sani yake ’yata, ba za ki samu biyan bukatarki ba har sai kin san jin dadinsa sama da naki, bukatunsa sama da naki, a dukan abin da kike so ko kike ki. Allah Ya zaba miki abin da ya fi alheri kuma Ya tsare ki.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.