Hikimomin zama da miji (7)

Dabara ta 5: Koyi da magabata, ci gaba… Darasi daga misali na biyu: Darasi abin dauka ga uwargida daga wannan misali shi ne dubi da yadda uwargida ta shimfida kyakykyawar nasiha ga ’yarta don ta zauna da mijinta lafiya, sannan in muka yi kyakykyawan nazari za mu ga cewa duk nasihohin suna nuni ne zuwa […]

Hikimomin zama da miji (7)

Dabara ta 5: Koyi da magabata, ci gaba…

Darasi daga misali na biyu: Darasi abin dauka ga uwargida daga wannan misali shi ne dubi da yadda uwargida ta shimfida kyakykyawar nasiha ga ’yarta don ta zauna da mijinta lafiya, sannan in muka yi kyakykyawan nazari za mu ga cewa duk nasihohin suna nuni ne zuwa ga karrama miji, mutunta shi da ba shi girma a matsayinsa na shugaba; duk da cewa wannan al’amari ya faru a lokacin Jahiliyya, babu tabbatuwar sakamakon shiga Aljanna ko wata muhimmiyyar lada kebantacciya, to ashe matan Musulmi su ya fi dacewa su dage da aikata wadannan kyawawan nasihohi domin bayan dace da samun kauna da mutuntawa daga maigida, da zaman lafiya, to kuma ga babban lada wacce ta fi komai ita ce shiga gidan Aljannar Ni’ima ranar gobe kiyama. Wani darasi abin dauka da dabbakarwa daga cikin wannan nasihohi na hakimar mahaifiya ga ’yarta shi ne, karramawa da girmama miji ana yi na yi da bari na bari,’ ko a ‘ladabi da biyayya’ kadai ya tsaya ba, ya shafi kusan kowane bangaren da uwargida ke mu’amalantar maigidanta. Yin murna da walwala lokacin da yake farin ciki da bayyana takaicin lokacin da yake bakin ciki, samar da abinci a kan lokaci, takaita hayaniya in yana barci, kyautata mu’amala da mutanen da suke karkashinsa, tattalin kayan masarufi da boye sirrinsa duk abubuwan nuna girmamawa da darajantawa ga maigida ne. Yin akasin haka kuma na nuna raini da rashin darajantawa ga maigida, wannan na nuna uwargida na sakaci da hanyar samun tsirarta ranar gobe kiyama. Da fatan Allah Ya sa mu dace da rahamarSa madaukakiya, amin.

Misali na uku: Sahabiyar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), Asma’u bint Abubakr (Radiyallahu Anhuma) ta ba da labarin kamar haka:

“Lokacin Az-Zubayr ya aure ni, ya kasance bai da gona, kuma bai da dukiya ko bawa ko wani abu makamancin haka, sai rakumi don debo ruwa da kuma doki. Na kasance ina kai dokinsa wajen kiwo, in ba shi dusa, in kula da shi kuma in nika dabino don rakuminsa. Bayan haka kuma ina kai rakumin wajen kiwo, in yi hada-hadar sama masa ruwan sha, in dinke gugar jan ruwan sannan in kwaba gari. Ban iya gasa burodi ba sosai sai dai makwabtana ke gasa mini sun kasance masu kirki. Sannan na kasance ina daukowa bisa kaina kwallon dabino daga gonar Az-Zubayr wacce Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ba shi mai nisan mil 2 daga Madina

Wata rana ina dauke da kwallon dabinon, na gamu da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai ya kira ni kuma ya umarci rakumarsa ta rusuna don in hau, sai na ji kunya in yi tafiya cikin gungun maza musamman da na tuna irin  kishin Az-Zubayr, don ya kasance mutum ne mai tsananin kishi. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fahimci kunya nake ji sai ya wuce abinsa (Sallallahu Alaihi Wasallam). Sai na zo ga Az-Zubayr kuma na labarta masa duk abin da ya faru, sai ya ce Wallahi, tunanin kin yi dakon ’ya’yan dabino ya fi mini ciwo sama da hawa rakuminsa (Sallallahu Alaihi Wasallam). Na ci gaba da rayuwa cikin wannan tsananin har sai da Abubakar (mahaifinta Radiyallahu anhu) ya aiko mini da baiwa wacce ta daukar wa ranta kula da dokin sai na ji kamar ta ’yanta ni.”

Darasin dauka ga uwargida shi ne kada asalinta da ya fi na mijinta, ko kudinta ko yawan albashinta da ya fi na mijinta, ko wani matsayi, daukaka ko fasaha da take da shi da ya fi na mijinta ya sa ta rika jin ta fi karfin ta yi masa girki ko ta wanke masa kaya ko kawo masa abinci in dai har da gaske tana son zama Musulma tagari. 

Dubi dai wannan labari na Asma’u bint Abubakar, mahaifinta shi ne Sayyidina Abubakar (Radiyallahu anhu), bayan kasancewarsa Babban Sahabin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), shi ne mafifici a cikin mutane gaba daya in ba Annabi ba; kuma ya kasance mawadaci, ta girma cikin wadatar mahaifinta amma wannan bai sa ta kasa hidima wa mijinta ba, bayan aikin gida da take yi har na gona da kula da dabbobinsa take yi. Amma a wannan lokacin wata ma ba ’yar kowa ba ce amma saboda ilimin boko da ‘wayewa’ sai ta ji tana jin nauyin yin dan karamin aiki ga maigidanta. Lallai matan aure ku tashi tsaye ku sake daura damara, ku cire girman kai, ku yaki Shaidan, burinsa ya kange ku daga more rayuwar aurenku karshe kuma ku rasa ladar yin ladabi da biyayya ga maigida, wato gidan Aljannar Ni’ima. Allah Ya datar da mu duka, amin.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.