Hikimomin zama da miji (8)

Alhamdulillah: Duniyar Ma’aurata ku cigaba da wannan kokari da kuke yi, a dalilin bayananku matata ta zo ta durkusa ta roke ni gafara in yafe mata abubuwan da take mini. A ranar 15. 04. 2018 filin duniyar Ma’aurata ya cika shekara 7, wannan shi ne burinmu a kodayaushe, ingantawa da kyautata rayuwar ma’aurata da jin […]

Hikimomin zama da miji (8)

Alhamdulillah:

Duniyar Ma’aurata ku cigaba da wannan kokari da kuke yi, a dalilin bayananku matata ta zo ta durkusa ta roke ni gafara in yafe mata abubuwan da take mini.

A ranar 15. 04. 2018 filin duniyar Ma’aurata ya cika shekara 7, wannan shi ne burinmu a kodayaushe, ingantawa da kyautata rayuwar ma’aurata da jin dadin zamantakewar aure. Ku cigaba da aiko da tambayoyinku ta whatsapp a wannan lamba: 08063675635, da kuma ta email da Facebook. Amsoshin tambayoyinku za su bayyana a wannan fili ne kadai, ba a bada amsa ta whatsapp, Facebook ko sakon sms. Da fatan Allah Ya taimake mu gaba d aya a kodayaushe, amin. 

Assalamu Alaikum. 

Matata tana zargina da rashin kula wajen ba ta hakkokinta na aure (ciyarwa,tufatarwa, mahalli da dai sauransu) wanda ya sa ita ma ta ga bai kamata ta ba ni hakkokina na aure ba. Wannan matsala ta dade muna fama ta ita har ta jawo mana saki a baya shi ya sa yanzu nake yin taka- tsantsa kar auren ya mutu kurmus alhali ga yara a tsakani.

Sha’anin rayuwa kullum abubuwa kara wahala suke har ya kai mu matsayin da matata ta rena samuna saboda ita ma tana da albashi. A shekaru 20 din da muke tare, na yi shekara 6 ba na aiki, musamman shekaru 3 yanzu a jere, amma na fada mata duk abin da ya dace ta yi da albashinta idan na samu aiki sai in biyata in kuma har mutuwa ta riske ni ban biya ta ba, to yana cikin bashi, don haka sai an cire mata a cikin abin da na bari kafin a raba gado.

A halin yanzu ba na aiki shekara 3 kuma ga halin da ake ciki, don haka komai ya tabarbare a tsakaninmu. Yau sama da shekara guda ke nan ba a taba yin sati daya ba sai ta ce in sake ta. Ta ce ita wannan aure zai kai ta wuta domin ita ba za ta iya yi mini biyayyar aure ba tun da na ki in dauki nauyin bukatunta gaba daya; yanzu haka ko magana ba ta yi da ni, yau wata 3 na bar gidan na yi yaji. Amma ina kiranta a  waya ba ta dauka, idan na yi sako ba ta cewa ta gani balle ma ta gode.

Ni da ita ba mu da iyaye kuma waliyyanmu duk sun rasu, don haka ba wani wanda za mu je gabansa ba tare da wani daga cikin mu ya ji ba a yi masa adalci ba. Don Allah mece ce shawara kuma ina mafita a wanan alamari?

Na gode.

Mafita: Duk inda aka samu matsala tsakanin mutum 2, musamman ma’aurata, to tilas su duka suna da kaso daga cikin wannan matsala, sai dai wani na da kaso mai girma wani nasa dan kadan ne, wani kuma shi ke kyasta ashanar da za ta ruruta wutar wannan matsala. Don haka hanya mafi sauki da saurin samun warware matsala ita ce kowanne daga ciki ya yi nazari zuwa ga tasa matsalar, ya amsa laifinsa kuma ya himmatu wajen gyarawa.

Maza su fahimci cewa Allah Ya sa ku a matsayin shugabanni ga matane a bisa sharudda biyu kamar yadda yaz o a cikin Aya ta 34, Suratun Nisaa’i: sharadi na 1 saboda falala Allah gare ku ta fanni kaifin hankali da hangen nesanku ya dara na mata, sharadi na biyu saboda kuna yi masu hidima daga dukiyoyinku. Don haka in ya kasance ba ku yin hidimar ciyarwa da sauran bukatu, hasali wasu matan suke ciyar da mazan da yi masu wasu hidimomin. A irin wannan zai yi wuya mace ta iya girmamawa da mutunta maigidanta, musamman in ya kasance yaren Soyayyarta shi ne a yi mata hidima da kudi, in ba a yi wannan ba to za ta ji kamar ba a son ta ne, an dauke ta ba a bakin komai ba. Musamman a wannan zamani da al’umma gaba daya ta rikice da bai wa kudi da mallakar wasu abubuwan more rayuwa muhimmanci sama da kyawawan dabi’u da kyautatawa. Don haka mai tambaya ka yi kokari ka cika wannan sharadi da zai ba ka dacewar zama shugaba ga iyalinka.

Sannan ka fahimci cewa ita mace halittar shaukiyya ce, don haka in ka fahimci abubuwan da take so, kana yi mata su, za ta mutuntaka da darajtaka ko ba ka da ko sisi. In mace ta tabbatar a cikin ranta cewa mijinta yana son ta kuma yana ganinta da daraja a rayuwarsa to zai mata sauki ta bi shi sau da kafa koda ba ta samu dukkan abubuwan bukatar ranta ba. Sai dai kowace mace yaren soyayyarta daban, in ya kasance matarka a yi mata hidima da dukiya, komai take so a sai mata shi ne ta fassara da ana son ta, to in dai ba ta kasance mai hakuri da iya lura da caccanzawar abubuwa ba, to kuwa za ku yi ta kai ruwa rana da ita, ba za ta taba amincewa kana son ta ba komai za ka yi mata in ba wannan da take so ba.

Sai sati na gaba Insha Allah.  Sauran bayanin amsar wannan tambaya na zuwa, insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos