Hikimomin zama da miji (9)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan hikimomin da uwargida za ta yi amfani da su don samun sauki da aminci cikin rayuwar aurenta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa […]

Hikimomin zama da miji (9)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan hikimomin da uwargida za ta yi amfani da su don samun sauki da aminci cikin rayuwar aurenta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

 

Mafita, cigaba daga makon jiya…

A makon da ya gabata bayani ya gabata ga mai tambaya game da yadda zai warware wannan matsala ta bangarensa. Ga bayani kan yadda za a warware wannan matsala ta bangaren uwargida:

Ga mata da Allah Ya jarrabta da kasancewar mazajensu sun rasa aiki ko sana’a, ko ya kasance sun fi mazajensu samu, da sauran yanayi makamatan wannan, hanya mai sauki kuma mai cike da alfanu ta yadda za ku zauna cikin aminci da mazajenku a wannan hali shi ne, yi don Allah da bari domin Allah.  taimakon da za ku yi a gida da iyali ko ga maigidan naku, ku kudira niyyar yi saboda da Allah. Kamar yadda Allah Ya yi umarnin fara bayar da sadaka ga mafi kusanci daga cikin mutane, in maigidanku ya kasance mabukaci, ku kuma mawadata, bayan iyaye shi ne mafi kusanci da yakamata ku taimakamawa kafin sauran ’yan uwa. In kuka rika yi domin Allah wannan zai tafiyar maku da kaikayin zuci game da rashin samun hidima daga mazajenku. Sannan duk wanda ya bayar domin Allah, Allah Zai nunnuka masa lada da kuma albarka cikin dukiyarsa. Hanya ta biyu ita ce in har ba za ku iya bayarwa gaba daya a matsayin sadaka ba, to sai ku bayar a matsayin bashi domin Allah, domin shim a bayarwa da karbar bashi ibada ce musamman in aka yi su kamar yadda shari’a ta tsara. Sai ki samu litttafi ana rubuta adadin kudin da kika kashe a kowace rana tare da shaidu da sa hannu, wannan sai ya zamar maki wani babban adashi duk ranar da Allah Ya sa maigida ya samu aiki ko sana’a sai ya biya.

Haka kuma ’yan uwa mata da suka samu kansu cikin irin wannan yanayi, ku sani cewa kima, daraja da daukakar ’ya mace ba a dacewa da miji mai dukiya da mallakar kayan more rayuwar duniya yake ba, kima da darajar ’ya mace yana cikin tsoron Allah da hali nagari. Ku yi tuni da cewa mafi daukakar matan wannan al’umma ba su rayu cikin daula ba, sun rayu cikin yau akwai gobe babu ne. Sannan da sun samu burin su shin e su bayar, su kyautar domin Allah. To ku yi koyi da haka ku rika daukar nauyin gidan a matsayin mijinku domin Allah, in dai kun kyautata niyya to rubi-rubin lada da alkairan da za ku samu ya fi a ce mazajenku na da wadatar yi maku hidima. Ku dubi misalin Uwar Muminai Nana Khadijah Radhiyallahu anha, dubi karramawar da ta rika yi wa mijinta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam duk da cewa ita Attajira ce, ta fi shi wadata, karshe ma ta sadaukar da dukiyar gaba daya don tallafawa mijinta, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam wajen yada Manzancinsa. Daga karshe dubi irin matsayin da ta samu a duniya da lahira.

Dubi misalin Nana Fatima Radhiyallahu Anha, dubi yadda ta yi zaman aurenta cikin halin hakurin yau akwai gobe babu, ko bai wa mai taya ta aiki ba ta da shi ita take ayyukanta gaba daya duk da cewa cewa Babanta shi ne Annabi kuma mafi daraja cikin halittun Allah gaba daya. A karshe dubi sakamakon da ta samu, ita ce shugabar matan Aljanna gaba daya. Dubi irin zaman da Matan Annabi Sallallahu alaihi wa Sallam suka yi, ta yadda sai a kwana ba a dora tukunya a wuta ba sai dai su ci dabino da ruwa. Don baka hakuri da jajircewa wajen bin dokokin Allah su ne daukakar mace ba wai rayuwar jin dadi da daula ba.

Sannan kuma a kiyaye, kar taimakon da kike wa maigida da dukiyarki, koda kin tsarkaka niyyarki ta zama don Allah kike yi, ya sa ki rika raina maigida kina masa gani-gani, in dai don Allah kike yi to ki girmama shi kamar yadda za ki masa idan ya kasance mawadaci kuma Ya tsare maki dukkan bukatunki. Da fatan Allah Ya sa mu dace da yin aiki da bari dominSa Azza wa Jallah, amin

Sai sati na gaba Insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.