Hisba ta cafke abokan da suka boye wata budurwa
Hukumar Hisba a karamar Hukumar Fagge da ke Jihar Kano ta kama wasu matasa abokan juna bisa zarginsu da laifin boye wata budurwa tare da yin lalata da ita. Matasan wadanda suka hada da Nura Gambo da Mutari Bala ’yan kimanin shekara 25, mazauna Unguwar Kurna sun boye yarinyar wacce aka boye sunanta tsawon mako […]
Hukumar Hisba a karamar Hukumar Fagge da ke Jihar Kano ta kama wasu matasa abokan juna bisa zarginsu da laifin boye wata budurwa tare da yin lalata da ita.
Matasan wadanda suka hada da Nura Gambo da Mutari Bala ’yan kimanin shekara 25, mazauna Unguwar Kurna sun boye yarinyar wacce aka boye sunanta tsawon mako uku inda suka rika lalata aikata da ita.
Rahotanni sun ce wadanda ake zargin sun gayyato wasu abokansu inda su ma suka yi lalata da budurwar.
Budurwar ta shaida wa Aminiya cewa matasan sun ajiye ta a wani gida da babu kowa a ciki, inda kuma suke kulle ta a duk lokacin da suka so fita waje. “Tun lokacin da na hadu da su suka ajiye ni a wani daki mallakar abokinsu inda na yi kwana uku a wurin. Daga nan kuma sai suka mayar da ni wani gida suka ajiye ni tare da yin lalata da ni. Haka
kuma sun gayyato wasu abokansu inda su ma suka neme ni. A duk lokacin da za su fita sai su kulle ni ta waje,” inji ta.
daya daga samarin mai suna Nura da ya yi magana a madadinsu ya ce “Lokacin da muka hadu da ita ta bayyana mana cewa ita bakuwa ce daga kofar kaura ta Jihar Katsina. Ta gudo daga gidansu ne sakamakon rashin jituwa da ke tsakaninsu da matar babanta. Sai na gaya mata cewa zan kai ta wajen Hukumar Hisba amma sai ta ki amincewa. Hakan ne ya sa muka ajiye ta a wani gida,’ inji shi.
Lokacin da yake tabbatar da faruwa lamarin Kwamandan Hukumar Hisba na karamar Hukumar Fagge, Salisu Umar Rijiyar Lemo ya ce wadanda ake zargin suna hannunsu yayin da daya daga cikinsu ya gudu.
Ya ce suna gudanar da bincike don gurfanar da wadanda ake zargi gaban kotu. Kuma a gefe guda suna kokarin gano iyayen budurwar.