Hisba ta cafke barawon yara a Kano
A makon jiya ne Hukumar Hisba ta damke wani mutum da ake zargi da fataucin kananan yara inda ya sayar da wani a kan Naira dubu 30.Darakta Janar na Hukumar Hisba, Alhaji Abba Sufi ya ce ma’aikatan hukumar tasu a karkashin ofishin Hisba na karamar Hukumar Gwale sun cafke mutumin ne a daidai lokacin da […]

A makon jiya ne Hukumar Hisba ta damke wani mutum da ake zargi da fataucin kananan yara inda ya sayar da wani a kan Naira dubu 30.
Darakta Janar na Hukumar Hisba, Alhaji Abba Sufi ya ce ma’aikatan hukumar tasu a karkashin ofishin Hisba na karamar Hukumar Gwale sun cafke mutumin ne a daidai lokacin da ya sayar wa abokin cinikinsa da ke zaune a Rijiyar Lemo cikin birnin Kano da wata yarinya mai kimanin shekara uku a kan Naira dubu 60.
Ya ce “Da muka bincika sai muka gano cewa wanda ake zargin ya dauki tsawon lokaci yana gudanar da sana’ar fataucin kananan yara, inda yake sayar da su a kan Naira dubu 30 zuwa dubu 60.”
Alhaji Sufi ya ce yawancin al’amuran da suka shafi fataucin mutane da Hukumar NAPTIP ke kula da su, tana samun su ne daga Hukumar Hisba. Haka kuma ya yi kira ga iyaye su sanya ido a kan ’ya’yansu don samun ingantacciyar al’umma.
Darakta Janar din ya cewa tuni hukumarsu ta mika wa Rundunar ‘Yan sandan Jihar lamarin don gudanar da bincike.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa tun farko an taba kama mutumin da laifin lalata kananan yara mata inda har aka daure shi a gidan maza na tsawon shekara biyu.
Kakakin Rundunar‘Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da cewa mutumin yana hannunsu, a yanzu kuma suna gudanar da bincike don gano wadanda suke sayen yaran a hannunsa. Haka kuma ya ce za a gurfanar da wadanda aka kama a gaban kuliya don hukunta su.