Hisba ta cafke fina-finan batsa a Kano
Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wasu fina-finan batsa da aka fi sani da (blue film) wanda aka shigo da su jihar ta barauniyar hanya. Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane wadanda ba a san ko su waye ba suka yi jigilarsu daga Jihar Legas don yin kasuwancinsu a Jihar Kano.Ustaz Aminu Ibrahim Daurawa […]
Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wasu fina-finan batsa da aka fi sani da (blue film) wanda aka shigo da su jihar ta barauniyar hanya.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane wadanda ba a san ko su waye ba suka yi jigilarsu daga Jihar Legas don yin kasuwancinsu a Jihar Kano.
Ustaz Aminu Ibrahim Daurawa shi ne Kwamanda Janar na Hukumar Hisba ya shaida wa Aminiya cewa hukumarsu ta yi nasarar kame wadannan fina-finan ne da taimakon wani fasinja wanda ke bin hanyar Legas.
“Wani fasinja ne ya sanar da mu cewa akwai fina-finan batsa da aka yi simogal dinsu a cikin wata mota da ke kan hanyar zuwa Kano. Ba mu yi kasa a gwiwa ba muka tura jami’anmu inda suka gano mana wasu jakunkuna wadanda suke cike makil da fina-finan batsa, inda yawansu ya fi 700.” Inji shi.
Kwamandan ya kara da cewa “Baya ga fina-finan batsa da ke cikin jakunkunan, hukumarmu ta cafke magungunan kara karfin maza da ke cikin jakunkunan, wato ire-iren magungunan da likitoci ke bayarwa ga irin mutanen da ke da rashin lafiyar gaba. Wannan yana nuna cewa masu wadannan kaya suna nufin su lalata mana tarbiyyar yara”. Inji shi.
Da yake jawabi game da irin matakin da hukumar Hisba ke shirin dauka a kan lamarin, Daurawa ya bayyana cewa zuwa yanzu ba su gano wadanda ke da alhakin shigo da fina-finan ba. “Zuwa yanzu ba mu gano masu fina-finan ba, amma duk lokacin da muka same su za mu yanke musu hukunci daidai da laifinsu. Ba za mu yarda mu zuba ido saboda abin duniyar da wasu tsiraru za su samu ta hanyar sayar da wannan fina-finai, mu kuma tarbiyyar ’ya’yanmu ta lalace ba. Kasancewar babu abin da ire-iren wadannan fina-finai ke koyarwa sai bata tarbiyya, domin a nan ne ake koyon zina da luwadi da madigo da sauransu. Haka kuma daga kallon wadannan fina-finai ake kara samun yawaitar laifukan fyade a cikin al’umma. A shirye muke mu dauki tsattsauran mataki a kan irin wadannna mutane” Inji shi.
Ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su zama masu kula da tarbiyyar ’ya’yansu ta hanyar sa ido a kan irin fina-finan da suke kallo, kasancewar matasa ne suka fi kallon irin wadannan fina-finai.