Hisba ta cafke tsoho da almajiri kan fyade
Hukumar Hisba ta Jihar Kano, reshen karamar Hukumar Dala, ta cafke wani tsoho mai kimanin shekaru 80 bisa zarginsa da yi wa wata yarinya mai suna Fabour ‘yar kimanin shekaru 7 fyade a unguwar Kurnar Asabe, babban layi.Aminiya ta rawaito cewa dubun tsohon mai suna dayyabu Amadu, wanda aka fi sani da Maikudi, ta cika […]

Hukumar Hisba ta Jihar Kano, reshen karamar Hukumar Dala, ta cafke wani tsoho mai kimanin shekaru 80 bisa zarginsa da yi wa wata yarinya mai suna Fabour ‘yar kimanin shekaru 7 fyade a unguwar Kurnar Asabe, babban layi.
Aminiya ta rawaito cewa dubun tsohon mai suna dayyabu Amadu, wanda aka fi sani da Maikudi, ta cika ne a makon da ya gabata, sakamakon kwanton bauna da mazauna unguwar suka yi masa, inda sai da suka tabbatar ya shigar da yarinyar cikin gidan, ya rufo kofa, sannan suka haura suka iske yana shirin amfani da ita.
Mahaifin yarinyar Mista Thomas ya bayyana wa Aminiya cewa a lokacin da lamarin ya faru ba ya gida, sai matarsa ta buga masa waya take sanar da shi halin da ake ciki, “Sai na yi gaggwar komawa gida, sannan daga bisani muka dunguma zuwa ofishin Hukumar Hisba”.
Ita ma yarinyar a nata bangaren, ta bayyana wa Aminiya cewa tsohon yakan yi lalata da ita ne bayan ya tura ta cikin gidansa, inda bayan ya gama abin da yake yi, sai ya ba ta Naira 20, ita kuma ta sayi awara da kudin. “Yakan kira ni gidansa, sai ya cire min wando ya kwantar da ni ya yi amfani da ni, sannan sai ya ba ni Naira 20, ni kuma nakan sayi awara da kudin”. Inji ta.
Tsohon, wanda ya ce shi dan asalin garin Dausayi ne a karamar Hukumar Ungogo, ya amsa laifinsa inda ya shaida wa Aminiya cewa wannan lamari kaddara ce ta fada masa saboda rabuwa da matansa biyu da ya yi tsawon lokaci. “Duk wannan abu ya faru ne saboda rashin iyalina, iyayen matana ne suka raba ni da su, bayan mun haifi ’ya’ya 11 da su, kodayake a yanzu saura guda uku. Ina neman afuwa”.
Sai dai tsohon ya nemi afuwar jama’a, duk da, a cewarsa, ba zai iya lissafa yawan yaran da ya lalata a wannan unguwa ba.
A wani labarin mai kama da wannan Hukumar ta Hisbar dai ta cafke wani almajiri mai suna Usman Yakubu, dan kimanin shekaru 16, bisa samunsa da laifin yi wa wata yarinyar gidan da yake barance fyade.
Mahaifin yarinyar mai suna Malam Sulaiman, wanda malamin wata makarantar allo ne a unguwar Adakawa, ya shaida wa Aminiya cewa mahifiyar yarinyar ta shaida masa cewa tana cikin gida sai ga ‘yarta Khadija (Sayyada) ‘yar kimanin shekaru biyu da rabi a guje ta shigo gida tana kuka tana nuna wandonta tana cewa zafi-zafi. Nan da nan sai ta yi hanzarin duba yarinyar, inda ta ga duk matuntarta a tsattsage ga kuma jini. Da ta tambaye ta wanda ya yi mata hakan, sai ta ce Usman ne.
Da yake yi wa Aminiya karin haske game da alakarsa da almajirin, Malam Sulaiman ya ce ba dan makarantarsa ba ne, sun hadu ne a dalilin sana’arsa ta sayar da ruwa. “Lokacin da muka fara sabawa da shi, sai na rika jin tausayinsa ganin yadda yake shan wahala wajen tallar ruwan don haka sai na samo mishi wani aiki inda ake biyansa Naira 600 a kullum, sannan idan ya dawo, sai ya dauki cincin din da mai dakina ke sayarwa ya fitar mata da shi kofar gida, inda take biyansa ladar tallarsa. Baya ga haka kuma a gidana yake cin abinci, sau uku a kullum”.
Almajirn, wanda dan asalin garin Maradi ne a Jamhuriyar Nijar, ya zo Kano ne don yin karatun allo, bai musanta laifin da ake zarginsa da shi ba, sai dai ya ce tsautsayi ne ya kai shi ga aikata wannan aika-aika.
Malam Abubakar Mati Salihu shi ne Mataimakin Kwamandan Hisba a karamar Hukumar Dala ya shaida wa Aminiya cewa hukumarsu ba za ta kyale mutanen ba, za ta gurfanar da su gaban kuliya don yi musu hukunci daidai da laifin da suka aikata.
Malamin ya bayyana cewa yawancin mutanen da ake kamawa da irin wadannan laifuka, ba ‘yan asalin karamar Hukumar Dala ba ne, amma ana tabbatar da an musu hukunci, don ya zama darasi ga na baya.