Hisba ta cafke ‘yan fim saboda amfani da yunifom dinta
A karshen makon da ya gabata ne Hukumar Hisba ta cafke wasu ‘yan fim din Hausa lokacin da suke daukar wani fim a gidan namun daji da ke Jihar Kano, sakamakon yin amfani da kayan hisbar ba tare da iznin Hukumar ba.An ce a lokacin wannan kamen hukumar Hisba ta kwace kayan aikin daukar fim […]
????????????????????????????????????

A karshen makon da ya gabata ne Hukumar Hisba ta cafke wasu ‘yan fim din Hausa lokacin da suke daukar wani fim a gidan namun daji da ke Jihar Kano, sakamakon yin amfani da kayan hisbar ba tare da iznin Hukumar ba.
An ce a lokacin wannan kamen hukumar Hisba ta kwace kayan aikin daukar fim da suka hada da kyamarori da fitilu da sauransu.
Daga cikin wadanda hukumar ta cafke akwai fitaccen dan wasa Sani Garba wanda aka fi sani da S. K , inda ya shaida wa Aminiya cewa suna tsaka da daukar fim din ne a lokacin suna sanye da kayan hisbar sai suka ga dakarun hukumar a kansu inda suka kama su suka tafi da su ofishin hukumar.
Barista Nabahani Usman shi ne mukaddashin Kwamanda Janar din hukumar ya shaida wa Aminiya cewa, hukumar ta sami labarin ne ta hanyar jami’anta na sirri, sun kama wadanda suka aikata hakan, “Lokacin da za mu sake su mun yi musu gargadin kada su kara aikata irin hakan a nan gaba. A yanzu haka ma sun rubuto mana wasikar neman gafara tare da neman iznin ci gaba da daukar fim din, sai dai a bangarenmu mun nemi su kawo mana labarin fim din nasu idan ya dace da ayyukan hukumarmu za mu ba su iznin yin amfani da kayanmu.” Inji Nabahani
Sai dai a tattaunawar da Aminiya ta yi da Shugaban kungiyar ’Yan fim ta Arewa (AFMAN) Isma’ila Afakallah ya yi tir da kamen da hukumar ta yi wa membobinsu, inda ya ce abu ne da ba ya bisa tsari wanda kuma a cewarsa ya keta doka. “A lokacin da aka kama mutanen nan suna daukar fim wanda kafin hakan masu shirya fim din sun riga sun samu izini daga ofishin hukumar da ke karamar Hukumar Gwale, sai dai akasin da aka samu shi Mataimakin Kwamnadan a ofishin bai mika kwafin takardar neman izinin ga hedikwatar hukumar ba. Abin haushin ma shi ne babu kokarin da kungiya ba ta yi ba wajen ganin an saki wadanda aka Kama din amma abin ya ci tura, sakamakon haka sai da suka shafe awa 32 a tsare. Wannan keta haddi ne, domin masu yin fim din sun sami iznin daukar fim dinsu daga Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano bayan ta gamsu da labarin da fim din ya kunsa. Ya kamata hukumomin biyun su rika gudanar da aikinsu kafada-kafada da juna amma ba su rika aiki a wawware ba.”Inji shi.
Afakallah ya ce ba su yarda da irin hakan ba.”Wannan shi ne karo na uku da Hukumar Hisba take kame mana mutane, mun ja hankalinsu a kan hakan amma ba su daina ba. Yanzu ta kai cewa duk wani wanda Hisba ta kama sai a danganta shi da sana’ar fim. Bari in yi amfani da wannan dama na ja hankalin wannan hukuma cewa abin ya ishe mu, haka, ma’ana ba za mu ci gaba da zuba ido muna fuskantar irin hakan daga hukumar ba, kuma za mu iya kokari wajen ganin an kawo karshen wannan al’amari ta hanyar bin hakkinmu a matsayinmu na ‘yan Najeriya.” Inji shi.
Game da matakin da za su dauka Afkallah ya ce zuwa yanzu kungiyarsu ta AFMAN tana tattaunawa da lauyoyinta a kan yiyuwar daukar matakin da ya dace.