Hisba ta kama dan sandan kan zargin yi wa budurwa fyade

Jami’an Hukumar Hisba a Jihar Jigawa sun kama wani dan sanda da ake zargin da yi wa wata budurwa fyade a lokacin da take yin wanka a ban-daki a gidansu.dan sandan mai suna danladi Abubakar mai matsakaicin shekaru mazaunin Unguwar Yalwawa da ke Dutse an ce ya shiga gidan su yarinyar ce (an sakaya sunanta) […]

Hisba ta kama dan sandan kan zargin yi wa budurwa fyade
Hisba ta kama dan sandan kan zargin yi wa budurwa fyade

Jami’an Hukumar Hisba a Jihar Jigawa sun kama wani dan sanda da ake zargin da yi wa wata budurwa fyade a lokacin da take yin wanka a ban-daki a gidansu.
dan sandan mai suna danladi Abubakar mai matsakaicin shekaru mazaunin Unguwar Yalwawa da ke Dutse an ce ya shiga gidan su yarinyar ce (an sakaya sunanta) a lokacin da ya gama bincike cewa ba kowa a gidan sai ita kadai sai ya shiga gidan kai-tsaye ya yi wa ban-daki tsinke saboda ya ji alamun ana wanka. An ce a lokacin ta shafa wa kanta kumfa sai ya yi mata shakar makauniya ya yi lalata da ita bisa tilas.
Bincike ya nuna wanda ake zargin direba ne a hedkwatar ’yan sanda ta Jihar Jigawa bangaren CIb.
Budurwar ’yar asalin Kaduna ce da suka dawo Jigawa tare da iyayenta saboda mahaifinta ma’aikacin gwamnati ne, shi kuma dan sanda da ake zargin makwabcinsu ne a Unguwar
Yalwawa da ke Dutse, kuma hakan ne ya ba shi damar kiwonta har ya kai ga yi mata fyade.
Kwamandan Hisba na Jihar Jigawa Ustaz Aliyu Limawa ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce wanda ake tuhumar sun mika shi ga ’yan sanda domin su gabatar da shi a gaban kotu don a yi masa hukuncin da ya dace.
Sai dai bayanai sun nuna dan sandan ya tsere ba ya zuwa wajen aiki, kuma jami’an Hisba sun ce saboda ma’aikacin kaki ne sun sanar da ’yan sanda laifin da ake zarhinsa da yi domin a kamo shi a yi masa hukunci.