Hisba ta kama mata 19 a samamen da ta kai wani gidan shakatawa

A karshen makon jiya ne Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kai sumame a wani wurin shakatawa da ke Tinshama a karamar Hukumar Nassarawa inda ta kama wasu mata da yawancinsu ba ’yan jihar ne ba.Bayanai sun ce dama wurin ya shahara kan ayyyukan badala inda da zarar dare ya fara sai ’yan mata da […]

Hisba ta kama mata 19 a samamen da ta kai wani gidan shakatawa
Hisba ta kama mata 19 a samamen da ta kai wani gidan shakatawa

A karshen makon jiya ne Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kai sumame a wani wurin shakatawa da ke Tinshama a karamar Hukumar Nassarawa inda ta kama wasu mata da yawancinsu ba ’yan jihar ne ba.
Bayanai sun ce dama wurin ya shahara kan ayyyukan badala inda da zarar dare ya fara sai ’yan mata da samari su rika kwararowa suna shaye-shaye da sauran ayyukan masha’a.
Mataimakin Kwamanda Janar na Hukumar kan ayyuka na musamman Barista Nabahani Usman ya shaida wa Aminiya cewa hukumar ta dade da samun labarin irin masha’ar da ake aikatawa a wurin, don haka bayan ta gama nazarin wurin ne ta yanke shawarar kai samame a karkashin jagorancin Sani Nasidi Uba (Remo).  “Tun da yamma muka tura jami’anmu na asiri zuwa unguwar inda suka samu nasarar kamo wadannan mata 19,” inji shi.
Barista Nabahani ya kara da cewa,”Tuni muka umarci likitocinmu su gudanar da gwaji a kan matan don tabbatar da lafiyarsu, saboda da dama wadanann yzra ba sa sanin cewa suna dauke da cutar kanjamau. Idan kun tuna a wani lokaci da muka yi irin wannan kame a Kwanar-Gafan mun samu mata 40 dauke da cutar kanjamau daga cikin mata 80 da muka kama. Muna yin wannan ne don mu kara nuna wa jama’a illar da ke cikin yawon banza, don su yi wa kansu da iyalinsu kiyamullaili.
Kwamandan ya ce bayan an gama gudanar da binciken likita, Hukumar Hisba za ta gurfanar da matan gaban kuliya don hukunta su don ya zama darasi ga saura.  
Wasu daga cikin ’yan matan da aka kama sun bayyana nadamarsu game da wannan hali da suka tsinci kansu a ciki. A cewar wata mace daga cikin wadanda aka kama mai suna Maryam “Na yi nadamar wannan hali da na samu kaina a ciki kuma insha Allah ba zan sake aikata hakan ba,” inji ta.
Ita kuma wata mai suna A’isha ta ce: “Ni ba wani abu ke kawo ni wannan wuri ba illa sayen kifi, ban san abin da ke faruwa a wannan wuri ba,” inji ta.