Hisba ta kama wasu matasa ba sa azumi a Kano
Hukumar ta ce za ta ci gaba da sa ido don tabbatar da cewar an kiyaye dokokin Shari’a a jihar.

Hukumar Hisba ta Jihar Kano, ta kama wasu matasa da ba su yi azumi a ranar farko ta watan Ramadan ba.
Mataimakin Kwamanda Janar na Hukumar, Dokta Mujahideen Abubakar ne, ya tabbatar da kama matasan.
Hakazalika, ya tabbatar da cewa jami’an Hisba sun cafke su yayin sintiri da suka yi a sassa daban-daban na Kano.
Har ila yau, hukumar ta kama wasu matasa ku san 60 bisa laifin askin banza, wanda ta ce ya saɓa wa dokokin addini da al’ada.
Bugu da ƙari, an kama wasu direbobin Adaidaita Sahu da ake zargi da cakuɗa maza da mata a cikin abin hawa, abin da hukumar ta ce ba za ta yarda da shi ba.
Hisba ta ce za ta ci gaba da sintiri domin tabbatar da an kiyaye dokokin Shari’a a lokacin watan Ramadan.