Hisba ta kama ‘yan bori a Kano

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wasu ’yan bori a lokacin da suke gudanar da borin a Unguwar Gwazaye a karamar Hukumar Kumbotso da ke jihar.Aminiya ta gano cewa al’ummar Unguwar Gwazaye ne suka sanar da hukumar kan yadda masu borin ke hana su barci a duk lokacin da suka tashi yin bikin nasu.Malam […]

Hisba ta kama ‘yan bori a Kano
Hisba ta kama ‘yan bori a Kano

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wasu ’yan bori a lokacin da suke gudanar da borin

a Unguwar Gwazaye a karamar Hukumar Kumbotso da ke jihar.
Aminiya ta gano cewa al’ummar Unguwar Gwazaye ne suka sanar da hukumar kan yadda masu borin ke hana su barci a duk lokacin da suka tashi yin bikin nasu.
Malam Sani Nasidi Uba Rimo, Mataimakin Kwamandan Hisba bangaren ayyuka da ya jagoranci kamen ya shaida wa Aminiya cewa sun kama mata da maza da kayan bori da suka hada da garaya da sauransu.
Sani Rimo ya ce a wancan kame ba su yi nasarar kame Sarkin Borin ba, kuma sun samu labarin ya ci gaba da gudanar da bori a unguwar. “A yanzu haka mun dauki matakin gurfanar da mutanen da ke hannunmu a gaban kuliya inda alkali ya sanya ranar 27 ga wannan wata don fara sauraren shari’ar. Shi kuma Sarkin Borin da muka samu labarin ya ci gaba da gudanar da borin za mu san irin hanyoyin da za mu bullo masa. Harkar bori harka ce ta jahiliyya mu kuma jiharmu jihar shari’a ce. Bori yana daya daga cikin laifuffukan da ba za mu yarda a ci gaba da gudanar da su ba,” inji shi.
Sani Rimo ya yi kira ga jama’a su rika sanar da Hukumar Hisba game da duk wani abu da ba su amince da shi ba, musamamn wanda zai tayar musu da hankali.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi