Hisbah sun kama karuwai 14 da kwace kwalaben giya 100 a Jigawa

Jami’an hukumar Hisbah ta jihar Jigawa sun kama karuwai 14 tare da kwato kwalaben giya 100 a hedkwatar karamar hukumar Kazaure  da ke jihar. An kaddamar da hukumar Hisbah a jihar ne don tabbatar da dokokin kasa. Kwamandan hukumar Hisbah Ibrahim Dahiru na jihar ne ya fitar da sanarwar, ya kuma ce an kama wasu […]

Hisbah sun kama karuwai 14 da kwace kwalaben giya 100 a Jigawa

Jami’an hukumar Hisbah ta jihar Jigawa sun kama karuwai 14 tare da kwato kwalaben giya 100 a hedkwatar karamar hukumar Kazaure  da ke jihar.

An kaddamar da hukumar Hisbah a jihar ne don tabbatar da dokokin kasa.

Kwamandan hukumar Hisbah Ibrahim Dahiru na jihar ne ya fitar da sanarwar, ya kuma ce an kama wasu mutum bakwai wanda adadin masu laifin ya kai 21.

An kama masu laifin ne a mashayar Gadar Kazaure.