Hisbah ta cafke dan-garuwan da ake zargi da kwartanci
Hukumar Hisba ta karamar Hukumar Dala a Jihar Kano ta cafke wani mai sayar da ruwa mai suna Isma’ila dambatta da ake zargi da bin gidajen matan aure yana yi musu fyade a unguwar Gobirawa.Mazauna unguwar sun ce dan-garuwan ya dade yana sayar da ruwa a unguwar, inda hakan ya ba shi damar sanin gidajensu […]
Hukumar Hisba ta karamar Hukumar Dala a Jihar Kano ta cafke wani mai sayar da ruwa mai suna Isma’ila dambatta da ake zargi da bin gidajen matan aure yana yi musu fyade a unguwar Gobirawa.
Mazauna unguwar sun ce dan-garuwan ya dade yana sayar da ruwa a unguwar, inda hakan ya ba shi damar sanin gidajensu da matan gidajen da yake kai ruwa.
A gidan da ya samu dama yakan yi wa mata fyade, idan kuma bai samu ba yakan tsoratar da su, domin an ce akwai wata mai ciki lokacin da ta gan shi a gidansu take ta haihu saboda tsoro.
Aminiya ta jiyo cewa dubun dan garuwan ta cika ne a lokacin da mutanen unguwar suka yi masa kwanton bauna suka kama shi a yayin da ya je wani gida don aika-aikarsa.
Wani mutum da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa “Kasancewar mun gane sai dare yake gudanar da wannan harka sai aka samu wani a cikin mutanen unguwar ya yi shigar mata ya kwanta a tsakar gida. Sai kuwa dan-garuwar ya haura gidan inda ya nufi wurin da yake kwance, kuma nan take mutumin ya cafke shi yana ihu. Hakan ya sa jami’an Hisba da mutanen unguwa da ke makale suka shigo gidan suka cafke shi.
dan-garuwan ya ce tsautsayi ne ya sa shi shiga wannan harka, domin a cewarsa wannan ne karo na farko da ya taba shiga wani gida a unguwar. “Wallahi wannan lamari tsautsayi ne ban taba aikata haka ba, ina neman afuwar jama’a,” inji dan garuwan.
Mataimakin Kwamandan Hisba na karamar hukumar Abubakar Salihu ya bayyana wa Aminiya cewa da zarar hukumar ta kammala bincike za ta gurfanar da shi gaban kuliya.