Hisbah ta cafke masu damfara da sunan aljanu a Kano
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta cafke wasu mutum hudu bisa zarginsu da laifin damfara, inda suke karbar kudin jama’a da sunan za su karba musu magani daga wani shugabansu da ke tare da aljanu.Dubun wadanda ake zargin ta cika ne a makon jiya yayin da suke gudanar da damfarar a Kasuwar Kachako, inda yaran […]
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta cafke wasu mutum hudu bisa zarginsu da laifin damfara, inda suke karbar kudin jama’a da sunan za su karba musu magani daga wani shugabansu da ke tare da aljanu.
Dubun wadanda ake zargin ta cika ne a makon jiya yayin da suke gudanar da damfarar a Kasuwar Kachako, inda yaran mutumin suke shiga kasuwa suna kiran jama’ar da ke da wata damuwa ko ta ciwo ko ta halin rayuwa domin su ba shi magani. “Da zarar sun gama jin damuwarka sai su faki idonka su sanar da shugaban nasu matsalarka, kana zuwa gabansa sai ya shiga zayyana maka abin da ke damunka ta yadda za ka yi saurin gaskata al’amurinsu ka ba su kudi,” inji majiyarmu.
Jagoran wadanda ake zargi da damfarar mai suna Muhammad Lawal Dutsinma ya ce “idan yaran nawa sun kewaya kasuwa suka samu abokan hulda sai rugo su sanar da ni matsalar mutane, daga nan idan matar ta zo, sai in bayyana mata duk abin da ke damunta, a matsayin aljanu ne ke gaya min. Jin hakan daga gare ni ke sama mutane suna sakin jiki tare da gaskata abin da nake gaya musu,” inji shi.
Muhammad Lawal wanda ya ce asalin sana’arsa ita ce sayar da magungunan gargajiya, ya ce sun dauki tsawon shekaru suna zuwa kasuwar don gudanar da wannan muguwar sana’a.
Malam Sani Nasidi Uba Rimo, Kwamandan Riko na Hisba a karamar Hukumar Takai ya
shaida wa Aminiya cewa sun mika matasan ga hedikwatar hukumar da ke Kano. “Zuwa yanzu Hisba ta tura wadannan mutane ga hedikwatarta da ke Sharada don ci gaba da bincike,” inji shi.
Jagoran ’yan damafarar ya yi nadamar abin da ya aikata, inda ya yi kira ga ’yan uwansa masu wannan sana’a su tuba su daina su nemi sana’a mai tsabta don gudanarwa.