Hisbah ta cafke mutum 37 kan karuwanci da sayar da giya a Yobe

Rundunar hadin gwiwar Hisbah da ’yan sanda da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta cafke karuwai dai masu sayar da giya a Yobe

Hisbah ta cafke mutum 37 kan karuwanci da sayar da giya a Yobe

Rundunar hadin gwiwar Hisbah da ’yan sanda da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta cafke wasu mutane 37 bisa zargin su da yin karuwanci da sayar da giya a Damaturu babban birnin Jihar Yobe.

Mukaddashin kwamandan Hisbah na jihar, Mohammed Murtala Goni Ahmed, ya ce an kama mutanen ne a Zango, Maina Lodge, Ajayi, Bakin Kasuwa da kuma Bakin Tasha a Damaturu.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin a ofishin rundunar ’yan sandan jiar, ya bayyana cewa mata 17 da maza 20 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 18 suka shiga hannu a samamen.

“Binciken da aka gudanar a kan wadanda ake zargin ya kuma nuna cewa, a cikin mazan, an same su da yawa suna sayar da kwayoyi sannan kuma an same su da kiret 50 na kwalaben giya,” in ji Goni.

Wasu daga cikin wadanda ake zargin da suka zanta da Aminiya sun ce an kama su ne bisa kuskure domin ba su da laifin abin da ake zargin su da shi.