Hisbah ta hana masu kwale-kwale lodi da tafiyar dare a Kano

Rashin kula ne ya janyo hatsarin kwale-kwalen da aka yi asarar rayukan mutane huɗu a Kano.

Hisbah ta hana masu kwale-kwale lodi da tafiyar dare a Kano

Hukumar Hisbah ta sha alwashin tura dakarunta wuraren da ake jigilar mutane da kwale-kwale domin ganin an magance yawan faruwar hatsari a faɗin Jihar Kano.

Hisbar ta ce daga yanzu ta haramta duk wani lodin mutane da ya wuce nauyin da ya kamata a ɗauka ko jigilar dare.

Mukaddashin Babban Kwanandan Hukumar, Dokta Mujahid Aminudden ne ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da manema labarai.

Dokta Mujahid ya bayyana cewa ɗaukar wanna mataki ya zama dole duba da yadda ake yawan samun hatsarin kwale-kwale da ke haddasa asarar rayuka da dukiya.

A cewarsa tuni Hukumar ta ba kwamandojinta na ƙananan hukumomi 44 da ke jihar umarnin tura dakarun Hisbah irin waɗannan wurare don ganin an fara aiki da umarnin kan lokaci.

Haka kuma dakarun Hiisbar za su sa ido don ganin ba a yi lodin da ya wuce ƙa’ida ba wajen ɗaukar mutane da kayansu a kwale-kwale.

Haka kuma ya ce dakarun Hisbar za su tabbatar cewa an daina tafiyar dare a kan ruwa.

“Za su tabbatar da cewa an daina ɗaukar mutane masu yawa a cikin kwale-kwale sannan kuma za su tabbatar da cewa da zarar ƙarfe 6:00 na yamma ta yi to ba za a sake ɗaukar mutane ba sai kuma gari ya waye.”

A cewar Hukumar Hisbar rashin kulawa ce ta haifar da hatsarin da ya auku a garin Kauran Mata a yankin Karamar Hukumar Madobi, inda mutane huɗu suka rasu yayin da har zuwa yanzu ba iya gamo mutane shida da suka nutse a cikin ruwan ba.

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana