Hisbah ta haramta sana’ar “downloading” a Kano

Hukumar ta sanar da ɗaukar matakin ne domin daƙile yaɗuwar munanan ɗabi’u a tsakanin matasa.

Hisbah ta haramta sana’ar “downloading” a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta haramta sana’ar tura fina-finai, wadda aka fi sani da “downloading,” a faɗin jihar.

Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne saboda wasu masu wannan sana’a na amfani da ita wajen yaɗa bidiyon batsa da sauran abubuwan da ke lalata tarbiyya.

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dokta Mujahid Aminuddeen ne, ya tabbatar da hakan a daren ranar Laraba.

Ya ce hukumar ta samu ƙorafe-ƙorafe cewa wasu masu sana’ar na yaɗa bidiyon baɗala da ke lalata tarbiyyar yara da matasa.

Ya kuma ce wasu mutane na fakewa da sana’ar wajen tura wa’azin addini, alhali a haƙiƙanin gaskiya suna yaɗa bidiyon da ba su dace ba.

Dokta Aminuddeen, ya ce hukumar ta tura jami’anta zuwa dukkanin Ƙananan Hukumomi 44 na jihar domin tabbatar da aiwatar da wannan umarni.

Ya ce yawancin abubuwan da ake yi a ƙarƙashin wannan sana’a sun saɓa wa koyarwar addini da kyawawan ɗabi’u.

Hukumar ta buƙaci al’ummar jihar su bai wa jami’anta haɗin kai wajen tabbatar da bin wannan umarni.

Ta jaddada cewar ta ɗauki matakin ne domin kare tarbiyyar yara da matasa tare da daƙile yaɗuwar abubuwan da suka saɓa wa addini da kyawawan halaye.