Hisbah ta haramta wa daliban Kano bikin ‘Candy’

Hukumar Hisbah ta haramta wa dalibai bikin kammala karatun sakandare da aka fi sani da Candy a Jihar Kano

Hisbah ta haramta wa daliban Kano bikin ‘Candy’

Hukumar Hisbah ta haramta wa daliban sakandare a Jihar Kano gudanar da bikin kammala karatu da aka fi sani da Candy.

Bisa alada dai dalibain da suka kammala rubuta jarrabawar fita daga sakandare kan gudanar da shagulgula don nuna farin cikinsu bisa ganin lokacin.

Da yake ganawa da manema labarai, Darakta-Janar na Hukumar Hisbah, Abba Sufi, ya bayyana cewa duba da yadda aka sami korafe-korafe game da yadda irin daliban suke nuna halaye marasa kyau da sunan murna, ya sa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci Hukumar ta dauki matakin da ya dace.

A cewar shugaban na Hisbah “Mun damu kwarai game da yadda yaranmu da suka kammala rubuta jarrabawarsu ta sakandare suke tayar da rigingimun a tsakaninsu.

“Wasu suna yayyaga kayan makarantarsu, wasu kuma suna bata su da rubuce-rubuce marasa amfani.

“A gaskiya wannan ba abu ne mai kyau ba.”

Sufi ya kara da cewa baya ga wannan kuma dalibai maza suna cudanya tsakaninsu da mata inda suke tafiya wuraren da bai kamata ba duk da sunan murnar kammala makaranta.

“Haka kuma ana samun daliban a wuraren da bai kamata a gan su ba.

“Wannan abu ne da Gwamnati ba za ta zuba ido ta bar shi yana ci gaba da faruwa ba,” in ji shugaban hukumar Hisbah.

Abba Sufi ya yi kira ga iyaye da su tsaya tsayin daka wajen sauke nauyin da Allah Ya dora musu na tarbiyyar ’ya’yansu.

Ya yi kira ga daliban da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’ar samun nasarar jarrabawar da suka rubuta a maimakon shigar da kansu cikin ayyukan sabon Allah.

“A matsayinku na dalibai kamata ya yi ku mayar da hankali wajen yin addu’a game da samun nasarar jarrabarwa da kuka rubuta.

“Haka kuma a maimakon ku yaga kayan makarantarku kamata ya yi ku ajiye wa kannenku sai su yi amfani da shi,” a cewarsa.