Hisbah Ta Haramta Wa Maza Yin DJ A Tarukan Mata a Kano

Sheikh Daurawa ya ce yin hakan ya zama dole don rage cakuɗuwar maza da mata a wuraren bukukuwa

Hisbah Ta Haramta Wa Maza Yin DJ A Tarukan Mata a Kano

Shiekh Aminu Daurawa

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta sanar cewa daga yanzu an haramta wa maza yin aikin DJ a tarukan mata a jihar.

Shugaban Hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya sanar da hakan ne a lokacin ganawarsa da ƙungiyoyin masu sanar kidi na DJ.

Malamin ya bayyana cewa yin hakan ya zama dole ne rage cakuɗuwar maza da mata a wurin bukukuwa a Jihar Kano.