Hisbah ta haramta yin kayan ‘na gani ina so’ a Sakkwato
Kazalika ta haramta sanya manyan lasifika a kan baburan Keke NAPEP, da kuma zaman mata a gefen direban Keke NAPEP
Bikin aure
Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato ta sanar da haramta wasu al’adu da ake yi a yayin bukukuwa da shirye-shiryen ɗaurin aure, tana mai cewa sun saɓa wa koyarwar Musulunci da kuma kyawawan ɗabi’u.
Daga cikin abubuwan da aka haramta akwai kayan na gani ina so, wanda aka fi sani da “See I Love”, wato al’adar da saurayi ke kai wa iyayen budurwa kayan sha, biskit, alewa, goro da sauran kyaututtuka domin neman auren ta.
Hukumar ta kuma haramta sana’ar kaɗe-kaɗen DJ da waƙoƙin Wazigidi a bukukuwa da kuma tarukan nishaɗi da maza da mata ke cakuɗuwa.
Kazalika ta haramta sanya manyan lasifika a kan baburan Keke NAPEP, da kuma zaman mata a gefen direban Keke NAPEP.
- Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta a Kano
- Wata 7 ba a biya mu haƙƙoƙinmu na samar da tsaro a Filato ba —’Yan sanda
Hisbah ta kuma haramta salon aski da ta bayyana a matsayin na marasa tarbiyya ga yara da matasa, da kuma tsaurarawa wajen yin kayan lefe.
Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato, Malam Usman Abdullahi Jatau, ya ce matakin ya fara aiki nan take, yana mai bayyana cewa an ɗauke shi ne domin kare kyawawan ɗabi’u da tabbatar da cewa ana gudanar da aure bisa koyarwar Annabi Muhammad (SAW).
Ya kuma gargaɗi masu shirya bukukuwa, masu sana’ar DJ da sauran masu ruwa da tsaki da su daina waɗannan abubuwa, yana mai cewa hukumar za ta ɗauki mataki kan duk wanda ya karya dokar.
Jatau ya kuma buƙaci iyaye da masu shirin yin aure su sauƙaƙa lefe tare da guje wa almubazzaranci, domin kauce wa basussuka da sauran matsalolin da ke tasowa sakamakon tsadar shirye-shiryen aure.