Hisbah ta kama masu badala 63

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta kama mutum 63 a wurare daban-daban a kewayen birnin Kano da ake zargi da aikata ayyukan masha’a iri-iri.Wadanda ake zargin sun hada da mata da maza da suke a tsakanin shekara 18 zuwan 30.Mukaddashin Babban Daraktan Hukumar, Barista Nabahani Usman ya ce wadansu daga cikin wadanda ake […]

Hisbah ta kama masu badala 63
Hisbah ta kama masu badala 63

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta kama mutum 63 a wurare daban-daban a kewayen birnin Kano da ake zargi da aikata ayyukan masha’a iri-iri.
Wadanda ake zargin sun hada da mata da maza da suke a tsakanin shekara 18 zuwan 30.
Mukaddashin Babban Daraktan Hukumar, Barista Nabahani Usman ya ce wadansu daga cikin wadanda ake zargin an kama su ne suna sayarwa ko shan giya a unguwannin da galibin jama’arsu Musulmi ne, wanda hakan bai dace ba.
Wuraren sun hada da Unguwar Hotoro da Zangon Dakata da Na’ibawa, kuma a cikin wadanda aka kama suna tu’ammali da barasar akwai Musulmi da Kiristoci. Ya ce tuni hukumar ta mika mutanen gaban Kotun Majistare ta yankin Nomansland a cikin birnin  Kano.
Haka kuma hukumar ta kama ’yan mata masu kananan shekaru da suke karuwanci a yankin Sabon Gari, a wuraren da suka hada da Titin Ibedi da Freetown da Titin Neja. ’Yan matan da aka kama bisa wannan zargin sun ka 37, kuma hukumar ta ce ta gurfanar da su a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke a Fagge ‘Yan Alluna kasancewar wadanda ake zargin Musulmi ne.