Hisbah ta kama masu yada bidiyon tsiraicin budurwa
Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato ta kama wasu mutum uku kan zargin yada bidiyon cin zarafin wata budurwa tsirara a intanet. A ranan Litinin hukumar ta tabatar da kama mutanen kan bidiyon da suka yada na budurwar da ake shirin yin bikinta a ranar 17 ga watan Oktoba mai kamawa. “Ranar 20 ga Yuni 2020 […]
Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato ta kama wasu mutum uku kan zargin yada bidiyon cin zarafin wata budurwa tsirara a intanet.
A ranan Litinin hukumar ta tabatar da kama mutanen kan bidiyon da suka yada na budurwar da ake shirin yin bikinta a ranar 17 ga watan Oktoba mai kamawa.
“Ranar 20 ga Yuni 2020 aka kira ni daga Legas kan bidiyon diyata tsirara ana cin zarafinta.
“Babban wanda ake zargin ya tura wa ma’aurinta diyata da wasu dandalin intanet bidiyon”, inji mahaifiyar budurwar.
- ’Yan bindigar da suka sace ’yan gida daya na neman miliyan N500
- Yadda ’yan Kannywood suka yi jimamin rasuwar Sarkin Zazzau
- ’Yan bindiga sun mayar da mata 22,000 zawarawa a Zamfara
Yaduwar bidiyon ya sa ma’aurin budurwa jingine batun auren wanda aka yi nisa da shirye-shiryen biki.
Kwamandan Hisbah na Jihar Sakkwato, Dokta Adamu Kasarawa, ya ce an kammala bincike kan wadanda ake zargin da suka hada da dan wani mai rike da mukamin siyasa da abokansa, za kuma a gurfanar da su a kotu.
Mahaifiyar budurwar ta ce babban wadanda ake zargin ya yi lalata da diyar tata ce a 2017 lokacin yarinyar tana da shekara 16 ya nada ya kuma adana bidiyon da ya yada da nufin lalata rayuwar yarinyar bayan samun labarin matsowar bikinta.
‘Hukumomi sun yi watsi da mu’
Ta yi korafin cewa duk kokarinta na ganin hukumar tsaro ta DSS da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa a Sakkwato su shiga cikin lamarin abin ya faskatra.
“Na yi takaicin rashin yunkurin hukumomin biyu”, inji ta yayin da take godiya ga hukumar Hisbah da ta shiga cikin lamarin.
Ta ce mahaifin wanda ake zargin ya nemi ya ba ta kudi ta janye karar, amma da ta ki sai ya yi ta mata barazana a lokuta daban-daban.
Kamfanin dillancin labaru na Najeriya (NAN) ya tuntubi Hayatu Tafida, mahaifin wanda ake zargin.
Ya ce yana da masaniya kan lamarin amma ya musanta yi wa matar barazana.