Hisbah ta kama matasan da ke sace wayoyi a gidajen biki

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da kama wadansu samari 10 masu shekara 13 zuwa 15 da aka zargin sun kware wajen sace-sacen wayoyin mata a gidajen aure da suna a birnin Kano. A yayin da jami’an Hukumar Hisbah suke gabatar da wadanda ake zargin da ke karkashin jagorancin shugabansu mai suna Ibrahim Ahmad […]

Hisbah ta kama matasan da ke sace wayoyi a gidajen biki
Hisbah ta kama matasan da ke sace wayoyi a gidajen biki

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da kama wadansu samari 10 masu shekara 13 zuwa 15 da aka zargin sun kware wajen sace-sacen wayoyin mata a gidajen aure da suna a birnin Kano.

A yayin da jami’an Hukumar Hisbah suke gabatar da wadanda ake zargin da ke karkashin jagorancin shugabansu mai suna Ibrahim Ahmad mai shekara 15, sun ce wadanda ake zargi da satar suna zaune ne a yankin Fagge dab da gidan Silima na Plaza, kuma sukan shiga cikin gayyar ’yan biki ne, kuma kasancewarsu matasa, matan bikin kan zaci dangin ango ne ko na amarya, don haka sai su saki jiki da su.
Matasan sun shaida wa manema labarai cewa sukan bi jakankunan matan ne su lalube tare da dauke wayoyinsu da duk wani abin amfani, su yi awon gaba da su.
Sun ce sun dade suna aikata haka ba tare da an gano su ba, inda suka ce a wasu lokuta har kari ko liki suke yi a lokacin shagalin biki, saboda yarda da su da aka yi da kuma kokarin sajewa da dangin ango ko amarya.
Shugaban matasan da ake zargi, ya ce “mukan yi amfani da kudin da muka samu daga satar wayoyin wajen sayen abinci, wani lokacin kuma mu sayi kayan wasa na talabijin.”
Ya ce da farko an fara kama mutum hudu ne daga cikinsu sakamakon kama shugaban ya saci wayar wata mace a wajen wani biki a Unguwar Fagge. “Mukan sayar da kowace waya tsakanin Naira 1500 zuwa Naira 2000, gwargwadon kyau da girmanta,” inji shi.
Ya ce galibinsu suna zaune ne a Unguwar Rijiyar Lemo da ke karamar Hukumar Fagge, amma sau da dama sukan kwana ne a Unguwar Fagge, kuma su suke ciyar da kansu da kudin wayar da suke sata.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi