Hisbah ta kama mutum 8 kan shirya zaɓen masu ƙwazon jima’i a Sakkwato

Hukumar Hisbah ta cafke wasu mutum takwas da ake zargi da shirya zaɓen gano waɗanda suka fi kowa ƙwazon jima’i a Jihar Sakkwato. Bayanai sun ce an gudanar da wannan ta’asar ce yammacin ranar Litinin a wani wuri mai suna Plus Centre da ke kan titin Maiduguri a birnin na Shehu. Rabon Awaki bai dace […]

Hisbah ta kama mutum 8 kan shirya zaɓen masu ƙwazon jima’i a Sakkwato

Hukumar Hisbah ta cafke wasu mutum takwas da ake zargi da shirya zaɓen gano waɗanda suka fi kowa ƙwazon jima’i a Jihar Sakkwato.

Bayanai sun ce an gudanar da wannan ta’asar ce yammacin ranar Litinin a wani wuri mai suna Plus Centre da ke kan titin Maiduguri a birnin na Shehu.

A yayin da kawo yanzu ba a bayyana ko su waye waɗannan mutane ba, wasu sojoji sun yi iƙirarin cewa mutanen da Hisbar ta kama abokan aikinsu ne.

Cikin wani bidiyo na kai tsaye da Mataimakin Kwamandan Hisbah na Sakkwato, Dokta Abubakar Usman Rabah ya fitar, ya ce kamen ababen zargin na zuwa ne bayan wasu bayanan sirri da suka tattara a kan faruwar lamarin.

Ya ce sun tura jami’ansu cikin fararen kaya zuwa wurin kuma suka tabbatar da faruwarsa da ke tsaka da gudana yayin da har har an kammala zagaye biyu na zaɓen.

Ya ƙara da cewa, a yayin wannan aikin ne kuma jami’an Hisbar biyu suka jikkata yayin da masu halartar masha’ar suka rufe motocinsu da jifa, yana mai cewa sun nasarar damke mutane takwas.

Dokta Rabah ya kuma gargaɗi wuraren taro da su guji bai wa ɓata gari mafaka ta yaɗa duk wani nau’in abun assha a jihar.

Wani babban jami’in Hisbar da ya zanta da Aminiya ya tabbatar da kama mutanen, yana mai cewa wasu sojoji sun yi iƙirarin cewa abokan aikinsu ne.

“Mun saba fuskantar wannan matsala, don ko a lokuta da dama idan mun yi ƙwacen barasa, sai a samu wasu sojoji su zo da sunan mallakinsu ce. Amma idan mun tsananta bincike sai mu gano cewa ba haka ba ne.”