Hisbah ta kama mutum biyar da ake zargi da Luwadi a Kano
Duk wadanda ake zargin sun haura shekara 20.
Babban Kwamandan Hukumar Hisbah na Jihar Kano, Sheik Harun Ibn Sina
Hukumar Hisbah da ke da alhakin dabbaka kyawawan dabi’u bisa koyawar addinin Islama a Jihar Kano, ta kama wasu mutum biyar da ake zargi da luwadi.
Shugaban Hukumar, Harun Ibn-Sina da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama mutanen da ake zargi a Unguwar Sheka da ke Karamar Hukumar Kumbutso ta Jihar.
- Buhari zai gana da duk Sanatoci 109 a daren Talata
- Majalisa ta ki amincewa da Onochie zama Kwamishinar INEC
Cikin sanarwar da Ibn-Sina ya fitar a ranar Litinin, ya ce wasu mazauna yankin ne suka shigar da korafi a kan wannan batu.
“Duk wadanda ake zargin sun haura shekara 20 kuma mun kama su ne a ranar 11 ga watan Yuli yayin wani simame na musamman da jami’anmu suka kai,” a cewarsa.
Ibn-Sina ya yi godiya ga mazauna yankin da sauran masu da ruwa da tsaki a harkokin tsaro da suka bayar da gudunmuwa wajen kama mutanen.
Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, Ibn-Sina yana bayyana takaicinsa kan matasan da aka kama da wannan zargi mai munin gaske.