Bidiyon Tsiraici: Hafsat Baby ta shiga hannun Hisbah
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar da kama matashiyar da Hisbah ta kama kan zargin yin bidiyon tsiraici
Hukumar Hisbah ta kama wata matashiyar ’yar TikTok, Hafsat Babu, kan laifin yin bidiyon tsiraici a Jihar Kano.
Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya sanar da kama Hafsat Baby, wadda ta yi ƙaurin suna kan yaɗa munanan abubuwa a Tiktok.
A safiyar Litinin Sheikh Daurawa ya fitar da bidiyon matashiyar a cikin wasu mata da hukumar ta kama ta tisa keyarsu zuwa ofishinta, sai dai bai yi ƙarin bayani ba.
Hafsat Baby ta shiga hannun hukumar Hisbah ne bayan da dambarwar bidiyon tsiraicin nata ya tayar da ƙura.
- APC ta lashe zaɓen Gwamnan Edo
- NAJERIYA A YAU: Alkiblar Da Edo Za Ta Fuskanta Bayan Zaben Monday Okpebholo
Bidiyon tsiraicin nata ya ɓulla ne bayan a kwanakin baya ta wallafa wani bidiyon tuba, inda ta sanar cewa ta goge duk miyagun abubuwan da ta yaɗa a shafinta na Tiktok.
A wancan lokacin, ta yi bidiyon ne bayan Hisbah ta kama ta, ta yi nasiha game da abubuwan da take yi a Tiktok.
A game da bidiyon tsiraicin, Hafsat Baby ta bayyana a cikin wani sakon sauti a Tiktok cewa tsohon bidiyo ne da aka yi sama da shekaru biyu da suka gabata.
A cewarta a sautin wanda ba a tabbatar da sahihancinsa ba, ba ta san yadda aka yi bidiyon ya fita duniya ba, domin ta riga ta goge shi daga wayarta kuma babu mahalukin da ta tura wa.
Ta ce wai, ta fito ne daga wanka ne ta ɗauki kanta a Snapchat, amma ba ta ajiye a wayarta ba, kuma ba wani tura wa ba.
Dambarwar bidiyon tsiraicin Hafsat Baby ta kunno kai ne bayan makamancinsa na fitacciyar ’yar TikTok, Babiana Queen of Update, wadda ta bayyana cewa wasu ne suka fitar da shi, bayan sun yi mata barazana don ta ba su kudi amma ta ki amincewa.