Dubun matashin mai shekara 25, Bala Haruna, ta cika ne a yayin da yake yunkurin safarar yarinyar da wata matashiya zuwa kasashen Larabawa domin aikin gida.
Mataimakin Kwamandan Janar na Hukumar, Dakta Mujahid Aminuddeen, ne ya sanar a ranar Juma’a, cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Alhamis a ɗaya daga cikin tashoshin mota na cikin birnin Kano.
Ya ce Bala Haruna, dan asalin Karamar Hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa, an kama shi tare da Fatima Safiyanu mai shekara 23 daga Daura a Jihar Katsina, da kuma Hasiya Haruna mai shekara 11 daga Kazaure a Jigawa.
A cewarsa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano yadda aka shirya tafiyar da kuma tabbatar da cewa an dauki matakin shari’a da ya dace. Ya ƙara da cewa hukumar ta mika wanda ake zargi da ’yan matan ga Hukumar Hana Safarar Mutane (NAPTIP).