Hisbah ta kama ’yan mata 16 da ake safarar su a Kano

Duk ’yan matan Hausawa ne za a kai su Legas inda daga nan za a yi safar su zuwa kasashen waje, in ji Hukumar Hisbah

Hisbah ta kama ’yan mata 16 da ake safarar su a Kano

Jami’an Hisbah a Jihar Kano sun kama wasu kananan yara ’yan mata guda 16 da ake shirin safararsu zuwa kasashen waje.

Hisbah ta yi nasara kama su ne a yayin da ake loda su a wata babbar mota a tashar mota da ke Unguwa uku zuwa Legas.

Mataimakin Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Mujahid Aminuddeen Abubakar ya ce, “jami’anmu da ke tashar motan ne suka kama kananan ’yan mata da ake kokarin safarar su ta Legas, inda daga nan za a wuce da su Jamhuriyar Benin da kasar Ghana.

“Abin da ke kai su Ghana shi ne a can ake musu takardun tafiya na bogi, wadanda ake amfani da su a rarraba yaran zuwa kasashen Laraba.

“Dukkansu kananan yara ne mata, ba su sani ba karshenta shi ke nan a can za su mutu ko a sayar da su a matsayin bayi ko a sa su karuwanci, sun zama bayi.”

Mujahid ya ce, “abin bakin cikin shi ne duk yaran Hausawa ne, tara ’yan Kano, hudu daga Katsina, biyu daga Jigawa, daya daga Borno.

“Idan suka tafi karshenta wasunsu ba za a kara ganin su ba, kuma wannan harkar ta saba doka. A da ta kasar Nijar suke bi, amma sun sauya dabara, sun koma bin manyan motoci a tashar Unguwa Uku. Amma muna da jami’ai da ke sanya ido a can ma,” in ji shi.

Daga nan sai ya yi kira ga iyaye da su rika sanya idanu wajen kula da tarbiyyar ’ya’yansu, su daina ruduwa da samun  kudi ko kowace hanya, wanda hakan ke jefa rayuwar ’ya’yansu mata cikin hadari.

“Bautar da ’yan matan ake yi idan aka fitar da su daga Najeriya, wasunsu a yi musu fyade, wasu a yanke sassan jikinsu a sayar, amma duk da haka mutane ba su daddara ba, wasu har miliyoyi suke biya wai don a yi safararsu,” in ji shi.

Sai dai bai bayyana ko an gano ko kuma an kama masu hannu a badakalar safarar ’yan matan ba, ko kuma yadda za a yi da yaran.