Hisbah ta kame mutum 48 tare da kwace katan 37 na giya a Jigawa
Hukumar Shari’ah ta Hisbah a Jigawa, ta ce ta kame wasu mutane 48 kan zarginsu da ta’ammali da giya tare da kuma kwace katon-katon na barasar 37 a yankin Karamar Hukumar Taura a Jihar. Kwamandan Hisban, Malam Ibrahim Dahiru shi ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse babban birnin Jihar, yau Talata. Malam Dahiru […]
Giya
Hukumar Shari’ah ta Hisbah a Jigawa, ta ce ta kame wasu mutane 48 kan zarginsu da ta’ammali da giya tare da kuma kwace katon-katon na barasar 37 a yankin Karamar Hukumar Taura a Jihar.
Kwamandan Hisban, Malam Ibrahim Dahiru shi ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse babban birnin Jihar, yau Talata.
Malam Dahiru ya ce jami’an Hisban sun cafke mutanen ne tare da hadin gwiwar ‘yan sanda, yayin wani farmaki da suka kaddamar a kauyen Gugunju.
Ya kara da cewar, a yayin samamen da suka kai, sun yi nasarar kame karuwai 30 tare da maza masu neman mata guda 18.
A cewarsa, sun mika wadanda ake zargin ga Hukumar ‘Yan Sanda dan bincike tare da gurfanar da su gaban shari’ah. Sa’annan ya kuma yabawa mazauna yankin musamman ma matasa a kan abin da ya kira bai wa Hukumar Hisban hadin kai, wajen gudanar da ayyukanta.