Hisbah ta lalata kwalaben giya miliyan 3.8 a Kano

Hisbah ta kwace tare da lalata kwalaben giya miliyan 3.8 a Jihar Kano a ’yan watannin da suka gabata

Hisbah ta lalata kwalaben giya miliyan 3.8 a Kano

Hukumar Hisbah ta kwace tare da lalata kwalaben giya miliyan 3.8 a Jihar Kano a ’yan watannin da suka gabata.

Kwamandan Hukumar, Dokta Harun Ibn-Sina, ya bayyana haka ne bayan hukumar ta sake kwace giya a unguwar Tudun Kalebawa da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a ranar Laraba.

Ibn-Sina ya ce hukumar tasa na samun nasara waje yaki da miyagun kwayoyi da kwacen giya da kuma yaki da miyagun dabi’u.

Ya bayyana cewa tuni Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da izinin lalata kayan da aka kama.

A lokacin da ake aikin lalata giyar, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya jaddada aniyar gwamantinsa ta kula da jin dadin jami’an hukumar Hisbah.

Ganduje ya halarci taron lalata giyar ne bisa wakilicin Dan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar Albasu, Sunusi Usman Batayya.