Hisbah ta ware wa ’yan jarida gurbi 50 a auren gata — Daurawa
Sheikh Daurawa ya ce makasudin ƙirƙiro tsarin auren shi ne kawar da baɗala a tsakanin matasa.
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi wa ’yan jarida albishir ɗin gurbi 50 a auren gata da za ta gudanar nan ba da jimawa ba.
Yayin ganawa da manema labarai, Shugaban Hisba na Jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce matakin ya biyo bayan nasarar da hukumar ta samu a auren gatan 1,800 da ta gudanar a baya.
- Harin Tudun Biri: Sojoji Sun Yi Ganganci —Hedikwakar tsaro
- Hajji: 15 ga watan Mayu za a fara jigilar maniyyata
“Mun bai wa ’yan jarida da sauran ma’aikatan kafafen yaɗa labarai da ke sha’awar shiga tsarin auren gurabe 50.
“Haka kuma mun shirya haɗawa da masu aiki a bangaren shari’a, da ma’aikatan lafiya domin tabbatar da an shigar da rukunin mutane iri-iri a tsarin,” in ji Daurawa.
Ya kuma ce makasudin ƙirƙiro tsarin auren shi ne kawar da baɗala a tsakanin matasa. Baya ga haka kuma haɗa aure tsakanin matasa na yaukaka alaƙa tsakanin al’umma da hukumar.
Daurawa ya kuma ce Hisbar ta haɗa guiwa da manyan makarantu da ke jihar, domin samar da makarantar bayar da horo da kuma koyar da dabarun ayyukan da suka shafi aikin hukumar, domin ɗabbaƙa ƙoƙarinsu na inganta al’adu da addini a jihar su kuma tafi daidai da zamani.