Hisbah za ta yi wa mutum 3,000 da za a yi wa auren gata gwaji a Kano
Hukumar ta ce dole ne duk wanda zai shiga tsarin sai ya tsallake matakin gwajin lafiya.
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta ce za ta fara gwajin lafiya daga ranar Litinin ga mutanen da aka zaɓa domin yi musu auren gata su 3,000.
Mataimakin Babban Kwamandan hukumar, Mujahideen Aminudddeen, ya ce duk waɗanda aka zaɓa daga Ƙananan Hukumomi 24 dole ne, su je ofisoshin Hisbah na yankunansu domin yin gwajin lafiya.
- Atiku ya caccaki Babachir kan kalamansa, ya nemi a haɗa kai a Najeriya
- Osinbajo ne ya kitsa sauke ni daga SGF, ADC ta sauya Atiku — Babachir
Gwajin zai haɗa da cututtuka kamar cuta mai karya garkuwar jiki, ciwon hanta, da gwajin dacewar jini (genotype), da kuma gwajin shan ƙwayoyi.
A tsakanin mata kuma za a yi musu gwajin ciki.
Jami’ai sun ce sai waɗanda suka tsallake gwajin ne kawai za su shiga tsarin yin auren.
“Za a ba da damar shiga shirin ne kawai ga waɗanda aka tabbatar suna da cikakkiyar lafiya,” in ji Aminudddeen.
Auren gata wani ɓangare ne na shirin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ke nufin aurar da maza 1,500 da mata 1,500, musamman mata marayu, zawarawa, marasa galihu da masu ƙaramin ƙarfi.
Kowane ango zai samu tallafin Naira 100,000 a matsayin sadaki, sannan ma’aurata za su samu kayan ɗaki kamar gadaje, katifu, kayan abinci da sauransu.
Haka kuma za su samu tallafin Naira 100,000 domin fara ƙananan sana’o’i.
Shirin na nufin rage wahalhalu, tallafa wa iyalai da kuma kawo zaman lafiya a jihar.
Duk da haka, wasu sun nuna damuwa kan yadda shirin zai ɗore a nan gaba.