Hisham Ali: Mutumin da ya ce yana jin harsuna fiye da 40

Aminiya ta ci karo da wani mai sana’ar daukar hoto a birnin Makka da ke kasar Saudiyya mai suna Hisham Ali wanda yake jin harsuna fiye da 40 na duniya . Daga ciki akwai Hausa da Turanci da Larabci da Faransanci da Indiyanci da sauran harsunan duniya masu yawa. Hisham ya koyi harsunan ne a […]

Hisham Ali: Mutumin da ya ce yana jin harsuna fiye da 40

Aminiya ta ci karo da wani mai sana’ar daukar hoto a birnin Makka da ke kasar Saudiyya mai suna Hisham Ali wanda yake jin harsuna fiye da 40 na duniya . Daga ciki akwai Hausa da Turanci da Larabci da Faransanci da Indiyanci da sauran harsunan duniya masu yawa. Hisham ya koyi harsunan ne a wurare daban-daban na kasar Saudiyya inda aka haife shi. Wakilinmu ya zanta da Hisham da Hausa da Turanci da kuma Larabci don ta tabbatar da ikirarin da ya yi, kuma ya kira ’yan wadansu kasashe kamar China da sauransu inda ya yi magana su da harsunan kasashensu a gabansa. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka?

Asssalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu. Sunana Hisham Ali. A birnin Makka aka haife ni kimanin shekaru 46 da suka wuce. Iyayena ma a Saudiyya aka haife su, amma kakannina a kasar Bangaladash aka haife su. Kakanmu ne ya zo Saudiyya ci-rani ya haifi iyayena su kuma suka haife ni. Ni ne na hudu a wurin mahaifiyata, amma ina da ’yan uwa maza da mata. Ina da mata daya da ’ya daya karama. Na yi makarantar firamare da sakandire a birnin Makka, daga nan ban ci gaba da karatu ba sai na shiga neman aiki, inda na yi aiki da wurare da dama da kuma kamfanoni daban-daban.
Aminiya: A wadanne wurare ko kamfanoni ka yi aiki?
Da yake ni dan kasa ne ina da takarda ban sha wahalar samun aiki ba. Na yi aiki da kamfanoni da dama, amma na fi dadewa a kamfanin gine-gine na Bin Laden, inda na shafe shekaru fiye da goma ina aiki a wurin. Daga nan na yanke shawarar shiga harkar kasuwancin sayar da kayan gini. Inda na samu aiki a shagon wani Balarabe da yake sayar da kayan gini. Ban dade ba na bar wurin saboda ba na jin dadi aiki a wurin. Sai na shiga harkar daukar hoto ta hanyar wani abokina. Shi ya koya mini yadda ake daukar hoto. Na koya har na sayi kyamara nake yi. Sana’ar daukar hoto nake yi har yanzu kuma na fi jin dadin ta saboda na fi samun ’yancin kaina a cikinta. Babu wanda yake takura mini. Sai lokacin da na ga dama in fito, in tashi lokacin da na ga dama.
Aminiya: Ga shi na ji kana magana da harsuna da yawa, har guda nawa kake ji?
Gaskiya mutane da yawa suna mamakin yadda nake magana da harsuna da yawa. Duk mutumin da ya zo wurina sai ya ji kawai ina yi masa magana da harshensa. Ba komai ya janyo haka ba sai in ce baiwa ce daga Allah. A yanzu harsunan da nake ji suna da yawa. Wadanda suka hada da manya da kanana. Ka ga ina jin Hausa wacce kake yi. Ina jin Turanci da Larabci da Indiyanci da Faransanci da Poshtu da yaren mutanen Philipines da na mutanen Indonesiya da na Bangaladash da yaren mutanen kasar Malesiya da yaren mutanen China da na Fasha da yaren Labanis da na mutanen Turkiyya. Larabcin ma ina jin na Yeman da na Saudiyya da na Iraki da na Sudan da Morocco da sauran yarukan da ba zan iya lissafa maka ba yanzu. Harsunan da nake ji sun fi 40.
Aminiya: Ta yaya ka koyi wadannan harsuna?
Ni kaina ba zan iya ce maka ga takamammen yadda na koye su ba, saboda ba zama na yi aka koya mini su ba. Amma abin da na sani shi ne na yi mu’amala da mutane a kamfanonin gine-gine masu yawa, musammam ma kamfanin gini na Bin Laden. A nan za ka yi mu’amala da kabilu masu yawa wadanda suka taho daga kasashe daban-daban. Ni abin da nake yi shi ne nakan kasa kunne ne in rika sauraren yadda mutane suke magana, da na saurara sai kawai in rika fahimtar yarensu. Daga bisani kuma sai in ji ina yin yaren ba tare da wata matsala ba. Baiwa ce daga Allah, ni kaina ina mamaki wani lokaci, mahaifana da ’yan’uwana da abokaina suna mamakin wannan al’amari. Mutane suna zuwa daga kasashe domin su gan ni kuma su gwada ni da yarensu. Kamar yadda kai ma ka zo don ka gwada ni. Na san kai ma ka samu labarina ne daga wurin wadansu Hausawa shi ya sa ka zo don ka tabbatar da gaskiyar maganar.
Aminiya: Ka taba tafiya wata kasa saboda ka koyi yare?
Gaskiya ban taba zuwa wata kasa ba saboda in koyi harshen mutanen kasar. Ban taba zuwa Najeriya ko Nijar ko Amurka ko Ingila ko Faransa ko Indiya ko Pakistan ko Turkiya ko Afganistan ba. kasar da na taba zuwa ita ce Bangaladash da Marocco. Bangaladash ziyara na kai don in ga ’yan’uwa kuma sau daya ko sau biyu na taba zuwa. Ita kuwa kasar Marocco kamfanin Bin Laden ne ya kai mu aikin gini. Kuma muna gamawa aka dawo da mu gida Makka. Sai dai babu lungun da ban shiga ba a kasar Saudiyya.
Aminiya:Ta yaya ka koyi Hausa?
Ai ni kusan zan iya cewa ni Bahaushe ne saboda a cikin Hausawa aka haife ni. A cikinsu na tashi, kusan ban da Larabci babu harshen da na fi iyawa kamar Hausa. Muna da hausawa da yawa a unguwarmu da muke kwana da su muke tashi. Ina da abokai da yawa a cikin Hausawa. Su kuwa sauran harsunan na ji su ne a wurin sana’ar daukar hotona. Don duk shekara masu zuwa aikin hajji da Umara suna zuwa ne daga sassa da dama na duniya da sun zo sai in rika sauraren yadda suke magana sai kawai in ji ni ma ina yi. Wato abin da na lura da shi shi ne Allah Ya yi mini baiwar da idan na ji yare sau daya sai kawai in rike, da haka sai kalmomin su rika taruwa cikin dan lokaci kadan sai kawai in iya.
Aminiya: Shin sauran harsunan kana jin su ne kamar yadda kake jin harshenka ko yaya abin yake?
A’a, jin harsunan ba ya zama daya. Na fi jin harshen mahaifana na Bangaladash da Larabci, sai kuma Hausa da na tashi a cikin hausawa. Amma sauran harsunan kamar Turanci da Faransanci da Sinanci (China) da sauransu, ba kamar yadda nake jin Hausa nake jinsu ba. Ita ma Hausa saboda kullum sai na yi magana da harshen ne saboda abokanan da nake da su a cikin hausawa.
Aminiya: Shin mene ne burinka a rayuwa?
Burina in cika da imani, in shiga aljannatul firdausi. In samu kwanciyar hankali da rufin asiri duniya da lahira. In samu zuri’a tagari da ’ya’ya masu albarka. Kuma in samu sana’ar da ta fi daukar hoto wacce zan samu arziki mai yawa in rika fitar da zakka da yin sadaka tare da taimakon jama’a.