Hissene Habre ya gurfana a gaban kotu a Senegal

Wata kotun musamman a kasar Senegal ta fara sauraren karar da aka kai tsohon Shugaban kasar Chadi Mista Hissene Habre, wanda ake tuhuma da aikata laifuffukan yaki da suka shafi cin zarafin dan Adam.A baya Mista Habre mai shekara 72 da kuma lauyansa, sun yi watsi da tuhumar kotun, inda suka ce kotun ba ta […]

Hissene Habre ya gurfana a gaban kotu a Senegal
Hissene Habre ya gurfana a gaban kotu a Senegal

Wata kotun musamman a kasar Senegal ta fara sauraren karar da aka kai tsohon Shugaban kasar Chadi Mista Hissene Habre, wanda ake tuhuma da aikata laifuffukan yaki da suka shafi cin zarafin dan Adam.
A baya Mista Habre mai shekara 72 da kuma lauyansa, sun yi watsi da tuhumar kotun, inda suka ce kotun ba ta bin ka’ida, saboda haka ba za su shiga cikin shari’ar ba.
Amma a ranar Litinin, Mista Habre ya halaraci zaman kotun, bayan da hukumomin kasar Senegal suka tilasta masa gurfana a gabanta
An dai kafa kotun ne bisa wata yarjejeniyar da kasashen Tarayyar Afirka suka kulla, kuma za ta saurari bahasi daga shaidu 100 a wannan shari’a da ake sa ran za a kwashe watanni da dama ana yi.
kungiyoyin kare hakkin Adam da wata kungiyar tabbatar da adalci a kasar Chadi, suna zargin Habre da laifin a kisan da aka yi wa fiye da mutum dubu 40 da ake dangantawa da siyasa da kuma azabtarwa a lokacin da yake mulki.
Hissen Habre ya shugabanci Chadi a shekarun 1982 da 1990, inda daga baya Shugaba mai ci a yanzu Idriss Deby ya hambarar da gwamnatinsa a wani juyin mulki.
Bayan hambarar da gwamntinsa ne ya yi gudun hijira zuwa kasar Senegal, inda aka ba shi mafakar siyasa, amma duk da haka kungoyoyin kare hakkin jama’a suka matsa don ganin a gurfanar da shi a gaban shari’a domin amsa tuhumar cin zarafin jama’a a lokacin mulkinsa.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos