Hizbullah: Sojojin Isra’ila sun kutsa cikin kasar Lebanon

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ta sha alwashin ci gaba da yakar kungiyar Hizbullah

Hizbullah: Sojojin Isra’ila sun kutsa cikin kasar Lebanon

Sojojin Isra’ila sun kaddamar kutse a Lebanon, a cewar gwamntin kasar Amurka a ranar Litinin.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ta sha alwashin ci gaba da yakar kungiyar Hizbullah tare da rufe wani bangare na iyakar kasar bayan ta kashe shugaban mayakan da ke samun goyon bayan Iran.

Ministan tsaron Isra’ila, Yoav Gallant ya yi gargadin cewa yakin bai kare ba, duk da wani gagarumin harin da kasarsa ta kai a birnin Beirut a ranar Juma’a wanda aka kashe shugaban kungiyar Hizbullah, Hassan Nasrallah.

Shugabannin kasashen duniya sun bukaci diflomasiyya da tsagaita wuta, yayin da mai magana da yawun Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, Stephane Dujarric ya ce: “Ba ma son wani hari na kasa.”

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ga, ya ce, jami’an Isra’ila “sun sanar da mu cewa a halin yanzu suna gudanar da ayyukan murkushe ayyukan Hizbullah a kusa da kan iyaka.”

Amma mataimakin shugaban Hizbullah, Naim Qassem, a jawabinsa na farko ta gidan talabijin tun bayan mutuwar Nasrallah, ya ce mayakan Hizbullah “a shirye suke idan Isra’ila ta yanke shawarar shigowa ta kasa.”

Wani soji ya shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP cewa Dakarun kasar Lebanon da mayakan Hizbullah suka rinjaya, suna mayar da sojoji nesa da kan iyaka.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon kuma ba su da ikon gudanar da sintiri “bisa la’akari da tsananin rokoki da suke kai da kawowa”, in ji shi.

Shugaban Amurka Joe Biden, wanda kasarsa ce kan gaba wajen samar da makamai ga Isra’ila, tun da farko a ranar Litinin ya nuna adawa da farmakin da Isra’ila ta kai a Lebanon.

“Ya kamata a tsagaita bude wuta a yanzu,” in ji shi.

A farkon wannan wata ne Isra’ila ta kai munanan hare-hare ta sama kan maboyar Hizbullah a fadin kasar Lebanon, kuma a ranar Juma’a ta kai harin bam a Nasrallah a birnin Beirut.

A Arewacin Isra’ila, kusa da kan iyakar Lebanon, Gallant ya ce “za mu yi amfani da dukkan hanyoyin da ake bukata… daga sama, daga teku, da kuma kan kasa” don dawo da kwanciyar hankali.

Ya ce kisan Nasrallah wani muhimmin mataki ne, amma ba shi ne na karshe ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Labanon ya ba da rahoton cewa, an kai hare-hare da manyan bindigogi a wani kauye da ke kan iyaka da ke kudancin kasar.