Hizbullah ta nada Naim Qassem a matsayin sabon shugabanta
Hizbullah ta nada Naim Qassem a matsayin sabon shugabanta, kasa da mako guda bayan rundunar sojin Isra’ila ta yi ikirarin kashe shi a harin jirgi sama.
Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta nada Naim Qassem a matsayin sabon shugabanta, kasa da mako guda bayan rundunar sojin Isra’ila ta yi ikirarin kashe shi a harin jirgi sama.
Hizbullah ta daga likafar Na’im zuwa matsayin shugabanta ne bayan rasuwar shugaban kungiyar Hassan Nasrallah da Isra’ila ta yi a watan Satumba a birnin Tehran na kasar Iran.
Kafin karin girman da ya samu, Na’im Qassem shi ne mataimakin shugaban kungiyar.
Sanawar da Hizbullah ta fitar ta ce an yi wa Na’im Qassem karin girma ne saboda yadda yake biyayya da tare-tsaren kungiyar sau da kafa.
- Lantarki: Za a gina babbar tashar ‘Sola’ a kowace jiha a Arewa
- Ba za a caji ’yan Arewa kudin wuta ba —Minista
A ranar Litinin ne manyan jami’an Hizbullah suka fuskanci hare-haren sojin Isra’ila.
A shafe watanni Isra’ila tana dauki ba dadi da Hizbullah, wadda ke goyon bayan kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas.