Hobbasar farfado da masakar KTL

Yau fiye da shekaru goma sha bakwai ke nan tun da wasu magidantan da yawansu ya haura dubu goma ke kwankwance a gidajensu, ba su da aikin yi don samun na rufin asiri ko daukar nauyin iyalansu sakamakon rugujewar masakun cikin garin Kaduna, wadanda suke taimakawa wajen ci gaban jihar  da kuma tallafar tattalin arzikinta. […]

Hobbasar farfado da masakar KTL

Yau fiye da shekaru goma sha bakwai ke nan tun da wasu magidantan da yawansu ya haura dubu goma ke kwankwance a gidajensu, ba su da aikin yi don samun na rufin asiri ko daukar nauyin iyalansu sakamakon rugujewar masakun cikin garin Kaduna, wadanda suke taimakawa wajen ci gaban jihar  da kuma tallafar tattalin arzikinta. An dade ana ta  ‘gafara sa,’ game da yunkurin da ake cewa ana yi don farfado da masakun ta yadda  ma’aikatansu za  su koma bakin aiki, amma ba wanda ya ga kaho ko kofaton san da ake cewa ana korowa.

To amma an ce komai ya yi farko zai yi karshe, ban da ikon Allah. Sai ga shi nan Allah cikin ikonsa Ya kawo mafita daga cikin matsalolin da suke hana farfadowar masana’antu da masakun cikin garin Kaduna. Jama’a kuma sun fara murna da jin haka, suna fatan ganin tabbatuwar haka cikin dan kankanen lokaci. Kamfanin NNDC, mai kula da masana’antun yankin Arewa da kuma zuba jari cikinsu  ya fayyace wa manema labarai a ‘yan kwanakin baya cewa an kawo karshen wahalhalun da masakar farko ta Jihar Arewa, watau Kaduna Tedtiles Limited (KTL) wacce aka kafa ta shekaru sittin da suka shude, ke fama da su.  Manajin Daraktan kamfanin NDDC, Dokta Ahmed Musa ya ce kamfanin, tare da hadin gwiwar wani kamfanin kasar Turkiyya, mai suna Sur Tedtiles  zai zuba jarin Dalar Amurka miliyan goma sha biyar a  masakar KTL.

Kamar yadda ya bayyana tsarin farfado da masakar,  kamfanin kasar Turkiya zai bayar da kashi talatin cikin dari na jarin da za a zuba, sa’annan kuma  masakar KTL da kanta za ta zuba jarin kashi arba’in da biyar cikin dari na jarin da ake bukata, ita kuma gwamnatin tarayya ta cikasa kashi ashirin cikin dari na sauran kudin jarin. Ba makawa yin haka zai taimaka wajen habaka arzikin Jihar Kaduna, ya kuma samar da aiki ga tsofaffin ma’akatan da ke da sha’awar komowa,  a kuma dauki  wasu ma’aikata masu sababbin jini a ciki da wajen Jihar Kaduna.

Duk da cewa dai ba a fayyace lokacin da  wannan jarin zai zo hannu ba, amma sai dai wani Babban Daraktan masakar KTL, Alhaji Abdullahi Gombe ya nuna cewa a yanzu kamfanin zai fara ne da aikin samar da  khakin da za a  dinka wa jami’an tsaro kayan sarki, kamar soja da ‘yan sanda da makamantansu. Haka nan kuma masakar KTL za ta nemi gwamnatocin wasu kasashen Afirka ta Yamma da su dinga sayen khakin dinka wa jami’an tsaronsu kayayyakin sanyawa.

Ita dai wannan masakar mallakar Gwamnatocin Jihohin Arewa goma sha shida ce, kuma Gwamnatin Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ce ta kafa ta a shekarar 1957, don ta dinga samar da tufafi da suturu iri-iri na maza da mata da ‘yan makaranta da kuma na jami’an tsaro. Kamfanin Marketing Board na Arewacin Najeriya ne ke bayar da kudaden sarrafa  masakar a karkashin wani kamfanin kasar Ingila da ake kira  Dabid Whitehead and Sons. A shekarar 2000 ce aka rufe wannan masakar sakamakon matsin da ya janyo kanfar kudi da kuma rashin wadatacciyar wutar lantarki mai karfin gaske da za ta murda tsofaffin injunan da suka tsufa, aka kuma kasa samun kayayyakin gyaransu, hatta ma a can kasashen da aka kekkera su.

A bisa gaskiya hangen nesan shugabannin yankin Arewa na farko ne ya kai ga kafa wannan masakar, kuma ba shakka ta taimaka wa wannan yankin a kokarin da ake yi na ciyar da shi  gaba da kuma habaka tattalin arzikinsa cikin hanzari. Masakar ta taimaka wajen raya harkokin kasuwanci da na zamantakewa a cikin garin Kaduna, kuma  yalwatar arzikin man fetur  daga shekarar 1970 zuwa 1997 ya kara habaka aikace-aikacen masakar da sauran irinta da ke Kaduna, mutane kuma sun amfana matuka da haka.

Sai dai matsalolin da suka yi ta afkowa a kasar a ‘yan shekarun baya ba su bar masana’antun yankin Arewa sun bunkasa yadda ake so ba, domin baicin rashin hana harkar sumogar tufafin da ake saka irinsu a kasar nan daga Indiya da kuma China, wasu hamshakan ‘yan kasuwa sun saye wasu masana’antun da ke mu’amala ko hulda da wadancan masakun, suka kuma rurrufe su, hakan kuma ya kara sa wahalhalun tattalin arziki sakamakon rashin aikin yi ga ma’aikata sun tabarbare ainun. 

Masakun kasar nan dai sun dogara ne ga audugar da ake nomawa a Arewacin kasar nan, to sai ga shi nan rashin mayar da hankali kan aikin gona ya sa manoma ba su iya noma audugar don rashin ribar da suke samu, sa’annan kuma wacce ake shigowa da ita don sarrafawa a masakun ta cika tsada, har hakan ya sa tufafin da ake  shigowa da su daga wasu kasashe  sun fi wadanda ake sakawa a nan ciki saukin kudi, kuma kowa ya raja’a a kansu. 

Sa’ilin da jama’a ke murna da wannan hobbasar da kamfanin NNDC na Arewacin kasar nan ya yi don farfado da kamfanin masaka na KTL sai a yi fatan gwamnonin jihohi da kuma hamshakan ‘yan kasuwa da dillan tufafi su ma za su hada gwiwa su samar da jarin da za a zuzzuba a sauran masakun don farfado da su. Babu abin da za su yi asara idan suka yi haka, domin kuwa yi wa wani yi wa kai ne. 

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara