Hodar Iblis: Kotu ta hana belin Abba Kyari

Kyari ya shaida wa kotu cewa tssare shi na shekara biyu kafin gurfanarwa ya saba dokar hukunta manyan laifuka har ga wadanda ake zargi da kisa

Hodar Iblis: Kotu ta hana belin Abba Kyari

Abba Kyari yayin zaman kotun na ranar Litinin

Babbar Kotun Tarayya da ke zama Abuja ta yi watsi da bukatar belin DCP Abba Kyari da wasu ’yan sanda hudu da ke tsare kan zargin hannunsu a badakalar safarar hodar iblis.

Da yake sauraron shari’ar a ranar Labara, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya ce wadanda ake zargin sun kasa gamsar da kotun kan dalilin da za ta ba da belin nasu.

Wadanda aka gurfanar din jami’ai ne a rusasshiyar rundunar musamman da ke yaki da masu garkuwa da mutane (IRT) karkashin jagorancin DSP Abba Kyari.

Abba Kyari da yaransa sun yi fice wajen yaki da kuma kama masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a sassan Najeriya.

Sauran mutane ukun da Hukumar Hana da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta gurfanar tare da Abba Kyari su ne Sunday J. Ubia, Bawa James, Simon Agirigba da kuma John Nuhu.

A ranar 14 ga Fabrairun 2022 NDLEA ta tsare DCP Abba Kyari kan zargin hannunsa a safarar hodar iblis daga kasar waje, a ranar 7 ga watan Maris kuma aka dakatar da shi daga aiki.

Mutane biyu — Chibunna Umeibe Emeka Ezenwanne — da aka kama sun shigo da hodar iblis din a filin jirgi na Akanu Ibiam da ke Enugu, sun amsa lafin, kuma an riga an yanke musu hukunci.

Amma Kyari da sauran jami’an na IRT sun musa laifin.

A sabon rokon da Kyari ya gabatar ya shaida wa alkalin cewa tsare shi na shekara biyu kafin gurfanarwa ya saba wa dokar hukunta manyan laifuka har ga wadanda ake zargi da kisa.

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji