Holland ta ki gayyatar Depay da Robin ban Persie

Tawagar kwallon kafa ta Holland ba ta gayyaci Memphis Depay da Robin ban Persie ba a cikin ‘yan kwallon da za su buga mata wasan sada zumunta da Wales. Wales ce za ta karbi bakuncin Netherlands a wasan sada zumunta da za su fafata a filin wasa na Cardiff a ranar 13 ga wannan wata […]

Holland ta ki gayyatar Depay da Robin ban Persie
Holland ta ki gayyatar Depay da Robin ban Persie

Tawagar kwallon kafa ta Holland ba ta gayyaci Memphis Depay da Robin ban Persie ba a cikin ‘yan kwallon da za su buga mata wasan sada zumunta da Wales.

Wales ce za ta karbi bakuncin Netherlands a wasan sada zumunta da za su fafata a filin wasa na Cardiff a ranar 13 ga wannan wata da muke ciki.
Depay mai taka leda a kulob din Manchester United da ke Ingila kawo yanzu ya zura kwallaye 19 a kulob din Manchester da kuma a kungiyar kwallon kafa ta Holland. Shi kuma Robin ban Persie da ke kwallo a kulob din Fenerbahce na Turkiyya kawo yanzu ya zura kwallaye biyar a raga daga wasanni 16 da ya yi a bana.
Sai dai kuma Netherlands din wacce ta kasa samun gurbin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai (Euro) da za a yi a Faransa a badi, ta gayyato Arjen Robben dan kwallon Bayern Munich da ke Jamus wanda ya warke daga jinya.
Wales ta samu tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da za a yi a 2016, kuma rabon da ta halarci babbar gasar kwallon kafa tun a kofin duniya da ta buga a shekarar 1958.

Yau Lahadi za mu sanya hannu a yarjejeniya da Iran — Trump

Za a yi jana’izar jagoran addinin Iran Ali Khamenei a watan Yuli

Fiye da ƙungiyoyi 60 sun yi zanga-zanga kan taron G7 a Faransa

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno