HOTUNA: Yadda aka yi shagulgulan Sallah a gida a wasu sassan Najeriya

Sallar Idin bana ta zo ma duniyar Musulmi a yanayi na annobar coronavirus, lamarin da ya sauya salon bukukuwan sallar bana,inda  a baya akan yi ziyarce-ziyarce sai dai a yanzu an gudanar da al’amuran sallar ne a gida. A Najeriya ma  jama’a da dama sun yi shagalin sallar ne a gidajensu tare Iyalansu, Aminiya ta […]

HOTUNA: Yadda aka yi shagulgulan Sallah a gida a wasu sassan Najeriya

Shahararen dan sandan Najeriya, mukadashin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari a lokacin da yayi shagulgulan sallah karama a gida tare da iyalinsa

Sallar Idin bana ta zo ma duniyar Musulmi a yanayi na annobar coronavirus, lamarin da ya sauya salon bukukuwan sallar bana,inda  a baya akan yi ziyarce-ziyarce sai dai a yanzu an gudanar da al’amuran sallar ne a gida.

A Najeriya ma  jama’a da dama sun yi shagalin sallar ne a gidajensu tare Iyalansu, Aminiya ta kawo maku hoton yadda aka yi irin wadandan shagulgula daga wasu jihohin Najeriya da suka hadar da Legas, Ogun dama  sassan Arewacin kasar.